Lyrics

Share ido ki bar yin hawaye amarya Sha kurumin ki angon ki ne, kunyi aure Da fari makaki Allahu na sanya a farko Wanda yayo shekara, yayi wata, yayi mako Dafa min Allah in sauke kayan dana dauko Na hangi amarya da ango yau take ranar aure Gida zaki je, haba-haba amarya Bikin naku ne, ki bar masu karya Ki dau shawarar iyaye amarya Ki mance zugar kawaye a baya Haba-haba amarya mai ladabi biyyayya Ki bi sahun mijin ki Amarya kiyi dauki Dan aljannaki Tana kafar mijin ki Rike hannu mijinki amarya ku tafi tare Naga daso a cikin sha'anin nan Har ta kai su ga aure Taci ado da asoke amarya har ta fesa turare Ki damke mijinki Shine jikon ki Ina makusan tan? Ku zo kuji zancen Rawa da alantan Da ni muku rance Waka da salon da yake taba zuciya ta amare Sha'anin aure riba ce Kin zama dauko riga Kin zama dauko hula Amarya dauko buta Toh ki sani aure bauta ne Babu fushi a zaman ku na kauna Amarya-aa-aa--aa-aa Amarya zauna Ga nan ku na tura Mun tayaki da murna Biki naki ake amarsu daure, daure Toh haka, haka Zo ku ji zan ce daga bakin Ado na gwanja Ni na karanta na nazarta kuma ina da hujja Aure nasara ce nasaba ce ba jani in ja Waka ado nake Sana'a ce na rike Da kai nake har da ke Baiti in nai rike Bana daki in dake Gumina ci nake Ban yarda a bi in tare Kama dai da wane ba ta wane Bikin yau na zo ina mata ne? Ku bude jakar kari daidai ne Gaku nan ga amarya Ga angon amarya Ga mawakin amarya Ina kawayen amarya? Abokai ku shirya Gaku nan ga amarya Kuyi rawa ku juya Ayi gaba ayi baya Kuma ku fidda kunya saboda ga amarya Albishirin ki yan mata albishirin ki Tashi ki juya kiyo rawa da bazar ki Na gano yan uwa da dangi na san ki Albishirin ki amarya ahir din ki Dauki tsararun kwarai cikin su kawayen ki Dan gudun karsu kai ki can haka su baro ki In ki kai haka sai muce kin ci garin ki Kin zama tilo cikin su kawayen ki Ba tambaya da ganin ki kinci sunanki Kiji ki kiki ji, ki gani ki rintsa ido amarya
Writer(s): Bello Hassan, Ado Isah Gwanja Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out