Lyrics

Eh lamari na duniya, wani ya samu wani yana kuka Mu munyi nasara, dan munyi hakar mu ya tarar da ruwa Lamari na duniya, wani ya samu wani yana kuka Mu munyi nasara, dan munyi hakar mu ya tarar ma ruwa Lamari na duniya, wani ya samu wani yana kuka Mu munyi nasara, dan munyi hakar mu ya tarar da ruwa Eh ita shinfidar fuska na tabbata ta wuce ta tabarma Itace aka yiman na mika wuya akasani a koma Wasu sunyi su nunan hanyar da zan gujewa nadama Sai yanxu nagane kyawun 'dan maciji ba kyawu ne ba Lamari na duniya, wani ya samu wani yana kuka Mu munyi nasara, dan munyi hakar mu ya tarar da ruwa Eh gudu na wahalta ke sa kaza taki cimar wake In amfani ne ice na madaci yafi na marke A batu na fatauci sanin haryarka saidai kafa sarki Shi mai lissafi sa hankali zaiyi na ba idanu ba Eh Lamari na duniya, wani ya samu wani yana kuka Mu munyi nasara, dan munyi hakar mu ya tarar da ruwa Eh duk mai yin kiwo in babu bajimi to bashida garke Toka aka sanya a cikin ruwa kunga dole a narke Shiko tauraro ado na samaniya 'karin haske Sirri na fahimta, sai an natsu ba cikin garaje ba Eh Lamari na duniya, wani ya samu wani yana kuka Mu munyi nasara, dan munyi hakar mu ya tarar da ruwa Lamari na duniya, wani ya samu wani yana kuka Mu munyi nasara, dan munyi hakar mu ya tarar da ruwa Eh hannu 'daya malam kyale baya iya 'daukar jinka A jikin minjirya na duba babu abincin kaska Nasan dai Jemage abinda yake 'kasa bai iya 'dauka Layi la shada bazaniyi bakar 'kudaje ba Lamari na duniya, wani ya samu wani yana kuka Mu munyi nasara, dan munyi hakar mu ya tarar da ruwa Eh mai kawo suka kunnen sa a bude yanasan gulma Babbar wata illa tasani gujewar hudo nama Hadamamme shine mai cuso kansa da kawo zalama Nasara har sa'a na nan in ban guji iyaye ba Lamari na duniya, wani ya samu wani yana kuka Mu munyi nasara, dan munyi hakar mu ya tarar da ruwa Eh kunsan in daji yakai daji ba a masa shuge Indai na dage jurewa haka zan cinma kurege Sai in na juya ko zaka saki mai yimani hange Ragamar damisa wazaya riketa bai dabarubba Lamari na duniya, wani ya samu wani yana kuka Mu munyi nasara, dan munyi hakar mu ya tarar da ruwa Eh lamari na duniya, wani ya samu wani yana kuka Mu munyi nasara, dan munyi hakar mu ya tarar da ruwa Eh lamari na duniya, wani ya samu wani yana kuka Mu munyi nasara, dan munyi hakar mu ya tarar da ruwa Lamari na duniya, wani ya samu wani yana kuka Mu munyi nasara, dan munyi hakar mu ya tarar da ruwa
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out