Lyrics

Sinadari na so makamashi Rura zuciyata suke yi A sannu sun zamo garwashi Kiyo agaji Sinadari na so makamashi Rura zuciyata suke yi A sannu sun zamo garwashi Kayo agaji Soyayya a zuci nake ruri kece zaki ban (makamashi) Hayaki wutar taki tashi ki tallafa kimin (makamashi) Kece kadai sinadari Zuciya take buri Karaso kizo da hanzari Kar in sha wuya Kishi in kina ji taho ga ruwa Babu mai taba ki tunda nine garkuwa Kaunar ki a duk jikina yayi yaduwa Babu kuskure in na kira ki kainuwa A duniyar masoya kin zam Sarauniyar cikin fadar Kici abinci kiyo dam-dam Muje mu rausaya Wannan halitta mecece? Ba'a gani da ido shin wacece? Hannu bai kama ta koko iska ce? Sai dai ka jita a jikin ka tayi kwance A suna an kira ta soyayya ce Ta shige jikina tayo kwance Ni kadai nasan ciwo na Damuwar cikin rai na Maganin ta sai watarana Wai yaushe zata zo? In babu ke a duniyar nan Sai dai in sha ruwan guban nan Zan more idan kina nan Farin ciki ya samu kenan Har abada bazan manta ki ba Kina cikin raina baki kaura ba Kece komai nawa Farin ciki na gani ga shi Sanyin ido nake kiran shi Ko zuciya tana yaba shi Kwayun halin sa bai da kyashi Sinadari na so makamashi (sinadari na so makamashi) Rura zuciyata suke yi (rura zuciyata suke yi) A sannu sun zamo garwashi (a sannu sun zamo garwashi) Kiyo agaji (kayo agaji)
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out