Top Songs By Nura M. Inuwa
Similar Songs
Credits
PERFORMING ARTISTS
Nura M. Inuwa
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Nura M. Inuwa
Songwriter
Lyrics
Ku gyara zama zana fada muku yau wasa an fara
Shanye rubutu hidima da kudi sai in an tara
Nayi rawata tai kyan kalla amma kan rera
Mai iya zance komai zai furta sai ya gyara
Shi gizo karya a kasan shi dayi magi ya kara
Gamu biki wanda ado mai kyau wane yar mora
Dan hidiman yau dole ka nema kudi
Inda zuma na gamsa dauka madi
San ya ido inda wata gefe zaka zaka gano zara
Dole ruwa za ya fito a jikin baure an sara
Shi rufa laya na badukku ne duba shi wajan kira
Za kaga kwaya a ciki na gyada inde ka bara
Neman sauki niyan tuba miyo kaffara
Nawa rabon ya rantse a ruwa na sama allura
Inda kazanta gu sai kaga 'kuda
Banda wurin yawo na zaba gida
Komai girman zakara a kace toro ya fishi
Banda abin dai kunne ya jiya wane yan amshi
In ka jiyo kukan gauraka taro ya tashi
Sai naji shago shi ne yaka shanye zafin naushi
Ko makaranta can baya ke 'kyele mai fashi
Jaddada kaifi na wukake ne tsini sai mashi
Madugu shi 'daya ke jure tafiya
Ga wani na ladabi dan gyara miya
Naga da ance aka yin shakar kamshi ko iska
Za aga haske fitila a duhu inde an haska
Mai magagi inde yaji feshi sai ya farka
Jaddada kalmar ga hawa sama tsani sai antaka
Cewa manoma su fito da Iri anyi ruwan shuka
Sanda ake so arufe daki ba'a bidar 'durka
Duk yanayi daya ne kwarya da duma
Gun kwari akushi ya dara su kuma
Kai mai wasa da biri shi ke burkata bakaka
Ga mafarauta da maciji nan kowa na shakka
Soja da kwazo ni sai na hange shi saman tanka
Gaida mazaje a wurin mata ne akasan dilka
Allah tsara tso-tsai a cikin waka in yaba hankaka
Karkayi burga da abin wani sai in ya zam naka
Cikar matsayin nono a hada da fura
In naci kifi bana shan madara
Illar aljan ka taba shi ka tun kari ma kwan cinka
To haka dodo ka taba shi a daji sai ya karka
Kayi gudu kakka du kani ka kakkare kukan ka
Ba wani motsi dan ba aikin yan sara suka
Ga mafita dai adu'a zakai baya jin duka
Gwanda ka roka duk inda kake shi sai ya jika
Ba nasara a gudu in ba mafita
Dukka na 'daure yana San yai sakata
Yara ku kamasu ku kaisu gida kura ta kwance
Dan mazari ya rike kan mota amma ta kwacce
Nuna iyawa da yake sanyi ya da san zarce
Sanya kulawa acikin tafiya rauni ka kauce
Duk mai zari baya hadama wannan ya dace
Nema kadan karka zu bawa baki sai ya huce
Kaji fushi baya kyawo ga damo
Nai magana kunne ya amsa awo
Nura da kyau karka sakar wa doki dukka limzami
Masu idanu sune suka gane girman rami
Masu gwalando su za su fada ma zafin fami
Tambaya yara dadin goyo raino sai momi
Duk maraji shine be san bari ba
Zanta zubo baiti ba zan gaji ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com