Lyrics

Hakanan anman sharrin maita Ana so sai an rabani da kai Ruwa indai da Alkawari yana da wuya ya cinye gwani Ehh Sharrin maita akaimaki kinji bar kuka kiyo hakuri Sanin haka shi yasani nake kiranki kibar yawan nazari Eh zamana dakai yana sa naji dadi Walwala ta ta rufe kaine mabudi Zanyi zaunawa dakai ko babu kudi Ayau anman sharrin maita ina fitila in ba lagwani Sharrin maita yanasa aitayin kuka rashin uzuri Yanasa 'dan gari ya fice ya kyale gari waye sanadi Karshe farko yake samo mafari Zabi kuma kishiya tai 'daiyi 'dari In an tafi sannu a ishe masu sauri Kibar 'daga hankalinki arai kisa hakuri yana magani Akaina yau akai sharri na maita Ya zauna man arai yazan na manta Ana bina ana neman makwanta Ina tsoron sharri baki gurina tinda ba lakani Eh kinsan ni baniso naga kinyi kuka Komai za'ace ki gane bani 'dauka Gonarki nike zuwa har inyi shuka Ni banida damuwa ana ace kallabi yaja rawani Tuwo kasan ba'a canzan shi suna Kallon mayya mutane ke wurina Komai ya faru ya 'kare ganina Rabewa nida dakai tilas rubuta za'ama izini Sharrin maita yanasa aitayin kuka rashin uzuri Yanasa 'dan gari ya fice ya kyale gari waye sanadi Mata ta zaki dawwama kau mafarki Gida na nan kikai dacen masauki Allah ya aminta wasu sunki Kina sona ina sanki batun araba mu daina tuni Sharrin maita yanasa aitayin kuka rashin uzuri Yanasa 'dan ya fice ya kyale gari waye sanadi Ehh Sharrin maita akaimaki kinji bar kuka kiyo hakuri Sanin haka shi yasani nake kiranki kibar yawan nazari
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out