Lyrics

Burin duniya na ganni a tare da kai Saudatu ce burin zuciya, ta shiga 'bargo har jijiya Al-'kawari dama na rika mai so na ba zan barta ba Kai ka zamo burin zuciya, ka shiga 'bargo har jijiya Dadi ko ma a cikin wuya, mai so na ba zan bar ka ba So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba In ta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai a cikin wuya Eh so ya sarke man zuciya, yabi jinina ya kewaya So datti in ban ganta ba, zan cigiya ko in tambaya Tinda na dakko al-'kawari, ko nai nisa zan waiwaya Saudatu kin zam raba gardama, wacce ta kai ke banganta ba So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba In ta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai a cikin wuya Tinda na same ta nasan, nai gamnakatar haka na anbata Ko da 'kishi sirrin ruhi ba a sani sai inya fita Rai na kama sai kaga kayi hakan so kayi mini bazata Yarda ka dauken haka nan nake, share hawaye na zai zuba So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba In ta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai a cikin wuya Eh 'kauna zahar tai sansani sai tafi karfin gangar jiki Dukkan rayuwa na barmaki ke kika zamto mai mallaki Aiki in zakiyi karki jira ki kirawoni mu taimaki Zan iya yin komai kirike wannan karki fargaba So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba In ta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai a cikin wuya So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba In ta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai a cikin wuya Eh kan so bashi baka bini ba kai nai nuni a cikin 'dari Da mun faro daga badini yayi yawa gashi a zahiri Domin neman dankon so waye yasa kaman kyautar yari? Na karba nai alfahari, duk tsanani bazan barka ba So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba In ta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai a cikin wuya Eh riba ta zama tare dake na yaba kyau naki da hankali Mai hakuri tare da tarbiyya mai samar da tawakkali Zanyi kula gun tare hakkin ki a gida zan zama adali Ga sarki nabi na sarauniya, ja ragamata tawu muje gaba So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba In ta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai a cikin wuya Eh nayo sa'ar babban rabo wanda dashi ban iya sa-in-sa Son sa ya kaudar da sukuni walla 'kiris ma in karasa Nayi aminci na gazgata so komai yana iya haddasa Ban da kamar kai nan duniya in dai har babu Uwa, Uba So sanadi mai sa zuciya, tayi gamo bada shirinta ba In ta fada in aka 'kiyi mata, ai tsintar kai a cikin wuya Saudatu ce burin zuciya, ta shiga 'bargo har jijiya Al-'kawari dama na rika mai so na ba zan barta ba Kai ka zamo burin zuciya, ka shiga 'bargo har jijiya Dadi ko ma a cikin wuya, mai so na ba zan bar ka ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out