Lyrics

Na fada maki sirrikan rai na gaskiyar zance ina sanki To kiyarda dani Na fada maka sirrikan rai na gaskiyar zance ina sanka To kayarda dani Na fada maki sirrikan Raina gaskiyar zance ina sanki To kiyarda dani So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana Bashida lakani Eh ra'ayi na ni soyayya, zuciyata yau kin sace Acikin 'kauna na dace, wasu nacewa na zauce Ita soyayya kurmace, notin kaina ya kwance 'kauna ta rinjayeni na 'dimauta saboda in sanki So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana Bashida lakani Eh ko akai zakaiman shaida, raina ansan ina sanka Tinda mun zauna mun saba, a cikin rai bana shakka Yi tunani gunka sai inji kamar ma ba tamkar ka Gudun 'bacin ranka nike koda wasa bana tsaki So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana Bashida lakani 'Karshen so dai aure ne kar kinyada miji naki Maganar ji ko zaki babu kamar abban 'ya 'yan ki Wanda in ranki zai gita, dake zaunawa 'daki In toshe masa garbu sila taso ba 'kwaron baki So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana Bashida lakani So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana Bashida lakani Ba arai in za'ayi baya abokin da ake sirri Tattali harda rukon da nake maka tamkar 'dan jariri A aminta da nagarta kai naiwa kallo na bugu 'kari Miji na ne kai zanaiwa batun danko a idon baki So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana Bashida lakani Eh a wani kogi nai nitsewa Gareni ba hanyar fitowa Ziran mayafi nai rikewa Jikina tsini kin cakawa Bani kaiwa in na cire sanki So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana Bashida lakani Ni nakai a masoyinki, in an 'daura mizanai Sama in zaki haurawa, ki kusanto nan ga tsani Duniyar nan an shela sanki bamai iya kamo ni Da Sarewa zanyo busa na hada maki harda ta kakaki So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana Bashida lakani Eh na fada maki sirrikan Raina gaskiyar zance ina sanki To kiyarda dani Ah na fada maka sirrikan Raina gaskiyar zance ina sanka To kayarda dani Na fada maki sirrikan Raina gaskiyar zance ina sanki To kiyarda dani So guda daya ba'a kasaptashi dan mutane biyu su amfana Bashida lakani
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out