Lyrics

Wata ruga, ruga, ruga Wata ruga Wata ruga na samo yarinyar fulani Ta shiga rai, burin da nake muyi aure Kai na sanar a soyayya zo jani-jani Wata ruga, zan koma in nayi aure Soyayya ce, soyayya ce Soyayya ta gare ki mai riba ce Nayo nazari kin yimin tantance Halin mu ya zo daya, haka sa'a ce Ni na shirya, zani sanya kiyi dariya Kema ki saka ni in zamo mai cin moriya Nayi rawar gani cikin soyayya Tun daga ke a yau na tako hanya Mu mun chaba mu ake kallo bai daya Ga yar fillo, gani dan Hausa guri daya Soyayya taka ce tasa rai na yayi fari Na kai matsayin da babu mai ce mini in bari In ba kai ba miya, ina ce maka gishiri Mai yin kushen ka ni da shi ba sauran shiri Ai sai murna ga wanda ya cika buri Kyautar Allah, babu mai maka gori Duk girman kogi, naga bai kin kari Na rike mulki, dole inyi kirari Bani canzawa a son ki nan ne na tsaya Zo taho tawa fulani ya mai kunya Kinyi burgewa da shigar ki sam babu haya Kin rike al'adar ki Shi ya kara mini son ki Wataran zamu wuce mataki Ran da zan zo in biya sadaki Ki zam iyali na A kai ki daki na Ki kare hakki na Da naki a guna In zana je gona Kiyi rakiya gu na Tunda kayi mini mai zai sa baza nayi ba? Inda soyayya ba abinda ba za'ayi ba Zanyi ma damu koda yaushe ba zan gaji ba Inda rai nasan da rabon mu ba zaya ki ba Kyan hali ne jarin ka dan Hausa Tarbiyya na nan a gidan Hausa Ka iya kalamai na ji tattausa Ayi auren mu ni fillo na kosa Wata ruga na samo yarinyar fulani Ta shiga rai, burin da nake muyi aure Kai na sanar a soyayya zo jani-jani Wata ruga, zan koma in nayi aure
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out