Lyrics

Eh lokaci yayi inda rai da rabo Madina kin dawo, ba kinyi nesa dani Madina tun farko ke nake ra'ayi Idan da rai da rabo karka yada ni Mutum yana tare da abinda yake so Shi rabon kwado bazaya hau sama ba Eh zuciya nazari aikin ta ne zance Afuwa ko zaba daka zans tantance Dan rashin ki Madina idanu suka 'kankance Kamarki nai hange bazani samu ba Mutum yana tare da abinda yake so Shi rabon kwado bazaya hau sama ba Eh kalma taso ga mutum 'daya ne wani ba'wa rance Mallakar abin so da zuciya kaga ai shine dace Gari na masoyi baya nisa ai hakika ce Nesa gata a kusa dani banyo zaton haka ba Mutum yana tare da abinda yake so Shi rabon kwado bazaya hau sama ba Eh allurai dake a cikin ruwa mai rabo shi yake tsinta Nai gamo nakatar nai tsintuwar adalar mata Ta mallakan zuciyar ta a hannu ta sakan zoben ta Rashi na wannan 'ya bazana so nai ba Mutum yana tare da abinda yake so Shi rabon kwado bazaya hau sama ba Mutum yana tare da abinda yake so Shi rabon kwado bazaya hau sama ba Dukka mai nazari lamarinsa shi yake dacewa So da kamar wasa a hankali ake farawa Wataran mu zame 'daya nida kai har mu sabawa Rukon amanata Allah sa baka gujen ba Mutum yana tare da abinda yake so Shi rabon kwado bazaya hau sama ba Eh wata rana ce nake ta jiranta tazaowa Sanadi na rashinki Madina na kusan zaucewa Na cire soyayya zuciya taki yarjewa Mai hakuri roman dutse bazai wuce sha nasa ba Mutum yana tare da abinda yake so Shi rabon kwado bazaya hau sama ba Ga amanar kaina ka rike karka kasawa Muyi zaman mu na aure nida kai muyi 'daurewa Tinda juna namu munaso anyi shedawa Innama laifi 'karami kadda kai duba Mutum yana tare da abinda yake so Shi rabon kwado bazaya hau sama ba Eh lokaci yayi inda rai da rabo Madina kin dawo, da kinyi nesa dani Madina tun farko ke nake ra'ayi Idan da rai da rabo karka yada ni Mutum yana tare da abinda yake so Shi rabon kwado bazaya hau sama ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out