Lyrics

Kuzo kuji tarihina labarina na Ado Yaro mai sharafi, sharafi, sharafi Kuzo kuji labari tarihin yaro Ado Yaro mai sharafi, sharafi, sharafi Ga tanan, ga tanan ku (tazo muji ta sharafi) To kusani dai a garin Kaduna state aka haife ni (yaro mai sharafi) Gari na mahaifa, Zango dai shine taken (yaro mai sharafi) Tun ina karamina abana yayi macewa (yaro mai sharafi) Allah ka jikan Ibrahim chan a kushewa (Allah ameen) Nagani da idona Tarzoma anyi gaba na (Allah ya kiyaye) Ina kallo an kashe yayena a gaba na (Allah ka jikansu) Sanadin hakane na koma Jos gun kawu na (yaro mai sharafi) Chan nai makaranta Boko harma islama Sharafi, sharafi, sharafi, sharafi Kuzo kuji labari tarihin yaro Ado Yaro mai sharafi, sharafi, sharafi Na kammala sakandare sai karatun yayi tsayawa (yaro mai sharafi) Ba aikin yi babu kudi da zanyi kashewa (yaro mai sharafi) Sai nayi tinani, in shiga fim din Hausa (yaro mai sharafi) Sai na tatara kayana na tafi tashan mota (yaro mai sharafi) Sai direba yace min wai ina zakaje Ado (yaro mai sharafi) Sai nace garin mai martaba sarki Ado Kanon dabo, koda me kaje an fika (yaro mai sharafi) Sai gani fage na sauka gidan inna ta Sharafi, sharafi, sharafi, sharafi Sharafi, sharafi, sharafi, sharafi Kuzo kuji labari tarihin yaro Ado Yaro mai sharafi, sharafi, sharafi A washe gari naje da kafata naje talawoto Palace of media, gun Salisu Mu'azu (yaro mai sharafi) Na same shi, Salisu yayi mini maraba (yaro mai sharafi) Ya bani abinci, naci nai nak ban manta ba (yaro mai sharafi) Bayan na huta yace "kai Adamu Zango" (yaro mai sharafi) "Me ya kawo ka, menene kazo yin nema" (yaro mai sharafi) Sai nace "oga nazo ne yin fim din Hausa" (yaro mai sharafi) "In zam kamar Ali Nuhu ko S Nuhu" (yaro mai sharafi) Sai yayi dariya yace "Allah zaiyi ma" Sharafi, sharafi, sharafi, sharafi Kuzo kuji labari tarihin yaro Ado Yaro mai sharafi, sharafi, sharafi A kwana a tashi sai gani ina yin kida (yaro mai sharafi) A kwana a tashi sai gani ina yin waka (yaro mai sharafi) A kwana a tashi sai gani a fim din Hausa Har nayi suna, na kere sa'ani na (yaro mai sharafi) Jamma'a sun sani domin kallon fim din Hausa (yaro mai sharafi) Kowa yasan ni idan yana jin wakar Hausa (yaro mai sharafi) Dole kasan idan kana jin kidan Hausa (yaro mai sharafi) A fage na kida, Daku shine oga na A fagen waka, Billy O shine oga na A fagen shirin Hausa Ali Nuhu ne oga na, sharafi Kuzo kuji labari tarihin yaro Ado Yaro mai sharafi, sharafi, sharafi Na zauna da mutane masu dunbin kaunata (yaro mai sharafi) Ali Nuhu (A zango yana gaishe ku) Hauwa MD (A zango yana gaishe ku) Salisu Mu'azu (A zango yana gaishe ku) Ibrahim Danko (A zango yana gaishe ku) Naziru Hausawa (A zango yana gaishe ku) Maryam Mash'ama (A zango yana gaishe ku) Khalil Germany (A zango yana gaishe ku) Khalid Kaciya (A zango yana gaishe ku) Falalu Dorayi (A zango yana gaishe ku) Mai gaskiya (A zango yana gaishe ku) Safiya Musa (A zango yana gaishe ku) Tijjani Asase (A zango yana gaishe ku) Tahir I Tahir (A zango yana gaishe ku) Baban Chenedu (A zango yana gaishe ku) Mika'l Gidigo (A zango yana gaishe ku) Umar Kanu (A zango yana gaishe ku) Auwal Isa West (A zango yana gaishe ku) Ghali Ali Basha (A zango yana gaishe ku) Masur Sadik (A zango yana gaishe ku) Lawal Ahmad (A zango yana gaishe ku) Tijjani Kazaure (A zango yana gaishe ku) Abubakar Sani (A zango yana gaishe ku) Jamilu Kazaure (A zango yana gaishe ku) Aminu Sulfa (A zango yana gaishe ku) Maryam Sangadale (A zango yana gaishe ku) Jamilan Sadi (A zango yana gaishe ku) Najasi SB Jakara (A zango yana gaishe ku) Abbakar hunter (A zango yana gaishe ku) Jamilu Kocida (A zango yana gaishe ku) Saifulahi (A zango yana gaishe ku) Muktar Uzzi (A zango yana gaishe ku) Sharu Nagudu (A zango yana gaishe ku) Lawan Alhassan Kaura Sharafi, sharafi Kuzo kuji labari tarihin yaro Ado Yaro mai sharafi, sharafi, sharafi Kuzo kuji tarihina labarina na Ado Yaro mai sharafi, sharafi, sharafi
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out