Lyrics
Gajimare kullum yana sama (kullum yana sama)
Tauraro ado a cen sama (ado ne acen sama)
Rana a sama itace girma (itace girma)
Kara hakuri farin wata
Bar Rana ta karkata
A daren duhu kayi 'bullowa
Gari ya 'dauki take da tambura
Kara hakuri farin wata
Bar Rana ta karkata
A daren duhu kayi 'bullowa
Gari ya 'dauki take da tambura
Rana ta fito gefen sama da hangenta kowa mikewa
Wani kasuwa wani sai gona ga ma'aikata na farawa
A sannu sannu rana take zuwa
Zafin ta garin nata hauhawa
Tsakiya da tazo ba natsuwa kowa yana inama ta gangara
Kara hakuri farin wata
Bar Rana ta karkata
A daren duhu kayi 'bullowa
Gari ya 'dauki take da tambura
Shi farin wata da daddare ne daya fito gari ya sangalce
Yara 'kana na adon gari da 'yan mata zance
Haske mai wuta sannu zai wuce
Bayan alfijir karku firgice
Rana da tazo ya kauce
Haske yakeso ya 'bantara
Kara hakuri farin wata
Bar Rana ta karkata
A daren duhu kayi 'bullowa
Gari ya 'dauki take da tambura
Kaji kwarjini da haskaka fitilar daba mai kangewa
Wata na nan a sama da rana kawai ke 'boyewa
Mi kake nufi cikin nawa
Mu muna jiran kai furtawa
Hanyar 'kwarai nake hangowa farin wata nake bi na makara
Kara hakuri farin wata
Bar Rana ta karkata
A daren duhu kayi 'bullowa
Gari ya 'dauki take da tambura
Bana bar batu gargadi nake duniya da rana ake nema
Yardar buwayi tana ga dare hasken wata hannin dama
Kan batun babu gardama
Amsarka sarai shin mai kadama
'Bullo watan samanyayi sama halinsa zayin amma yaci tira
Kara hakuri farin wata
Bar Rana ta karkata
A daren duhu kayi 'bullowa
Gari ya 'dauki take da tambura
Kara hakuri farin wata
Bar Rana ta karkata
A daren duhu kayi 'bullowa
Gari ya 'dauki take da tambura
Zuciya kamar zata fashe dan tunani na zautu
Kullun tunanina duniya daga kukukun ta na 'dan entu
Kara hakuri karka karkatu
'Dan Adam da buri zaya mutu
Randa babu ni nai hutu, Rabbi sa akanka nai nasara
Kara hakuri farin wata
Bar Rana ta karkata
A daren duhu kayi 'bullowa
Gari ya 'dauki take da tambura
Kai ki maidani farin wata da duhun dare bai 'boye ni
Rabbi karka sata hanya ta jama'a su hallaka kareni
Nasara kanima tarindini
Tambaya ina kabaro tsani
San Mustapha agareni farin watan da rana take jira
Kara hakuri farin wata
Bar Rana ta karkata
A daren duhu kayi 'bullowa
Gari ya 'dauki take da tambura
Kara hakuri farin wata
Bar Rana ta karkata
A daren duhu kayi 'bullowa
Gari ya 'dauki take da tambura
Lyrics powered by www.musixmatch.com