Lyrics

Tunda ta kwalla tazo Da mai kunbo Muka dau yayi Anan muka kyale fanteka Yar banza Aha, toh fah Kai nace, "Tunda na dau kwalla" Na dau kunbo Naci alwashin sai ci ubanki Fanteka, yar banza Kai nace Idan daya ce farko a lissafi Dole abi ta abar batun chanfi Kai mai yi shi yaga gaskiyar tsafi Amma kuma mai kwanon sha Yafi mai kofi Sai dan danbe yake batun shafi Hayaya shi kuma wanzam Bashi son yarfi Nace Ado Gwanja ne kubar haufi Kuma nasan zaku gano ni Wata rana Allah ne ya nufa nake waka Dole a garin a gani akan bar ni Wanda ya dauki zare yake saka Bani kiran sana'ar sa mai muni Shi kuma wanda ya saba Kirani dan kuka Shi yake guzurin kalma Marar dadi ya jefe ni Amma ni dana san Halin mutanen mu Bana jin haushi Idan sun kushe hali na Nazama rimi nazamo gamji Gwanja nayi kama da kan daki Allah ne ya nufa ace nine Ado Gwanja Ku kuma menene na mamaki Dole abar fitila da alkuki Mai gona bai raina mai taki Wanda yasan haushi yasan haushi Ba daya ne ba gurin rubutu ne Asali na Babu hadin saka da mai kuda Shi ko makeri bashi yin fida Ai yanayi shine yakan sauyi Mai cinikin danye ya dau koda Toh ku tsaya in baku labari Sai a bikin mata ake guda Karku ga dan na zagi fanteka Kuji haushi Ita tabar ni na bar ta Ga silver a hanuna Nace, ko kuji wai Ko kar kuji wai Da ku so da kuki Da kubi da kubar ni Idan naga rana dole nai shanya Rabbi yaso kuma yadda yaso Kuma sanda yaso Haka za'a ji za'a aga Babu batun tara da alkunya Kowa kar ya rufe tinanin sa Nace ba'a tare su ruwa akan hanya Idan nabi sakona ina bita A'a zai je inda naso cikin tsari Wata rana Ni da masoyana nake harka Tinda idan na fada suna shauki Kuko magauta kuta yin zagi Ko a tanan kune naba aiki Kuko kuna kallo ina waka Nazama fili kare gudun doki Mai kasani harma ka zage ni Kai in ka kai ma a zage ka Wata rana
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out