Music Video

Ali jita - Amarsu
Watch {trackName} music video by {artistName}

Featured In

Credits

PERFORMING ARTISTS
Ali Jita
Ali Jita
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Ali Jita
Ali Jita
Songwriter

Lyrics

Amarya share hawaye bar kuka Amarya ga kidanki kin farka Kinga aure shi yasa ki kin girma Arziki ne a duniya ake nema Inda kauna zaman gidanki ba fama Addu'a ta Allah ya kare yan gulma Babu wai wai mijinki gashi mai girma So da kauna shi yasa da alfarma Shi yana sonki kin aminta ai kema Shimfidar fuska ta wuce ta tabarma Sannu amarya gidan miji akwai dadi Kinga amarya a zantukanmu ba kaudi Kiji amarya kar batunmu yai fadi Karki damu babu sidi ba sidi Babu karya cikin gyada akwai gardi Mai misali kantu yake kira ridi Naji labari a baya anka sha fama Da magauta da tsegudidi yan gulma Kwanci tashi sun sallama a yau suma Rayuwa ce haka duniya ake fama In fada ne nasara tana wajen kurma Anyi auren magauta sun sani suma Har wa yansunsu sun shigo bikin suma Ga ido fes a zuciya suna kuka Ba kamanni farin sugar cikin laka Ga hakora ga zuciya tana tuka Yanzu an kammale ginin ana jinka Amarya amarya lokaci yayi Ke Amarya amarya zamani yayi Mu muna dariya wadansu na kuka Munbi Allah su sun biyewa yan girka Addu'armu muke su suna biye boka Lokaci ne kowa da lokacin sa Zamani ne kowa da zamanin sa Ai kamar wane kunga bata wane Mai abin biki dan yaje biki ne Mai karatu ganin mu malami ne Mai kwatance ganin mu dan gari ne Da kunga qura zuwa na ayari ne Toh arziki dai ashe jinin jiki ne Kuma mijinki mun gane jarumi ne So da kauna sanadin farin zama ne Sannu amarya amarsu lokaci yayi Sannu amarya amarsu zamani yayi Daina kuka mijinki ba rago ba Kumah bazai karya dukka alkawar ba Kumah bazai sha idan baza ki sha ba Kumah bazai bacci in idonki bai ba Kumah bazai kwana inda babu ke ba Ya ce, "Ba zai kara miki kishiya ba"
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out