Top Songs By Tasiu Unguwa Uku
Credits
COMPOSITION & LYRICS
Tasiu Unguwa Uku
Songwriter
Lyrics
Kura daban da kora
Dauri daban da dauri
Amma wurin rubutu kalmomin na kama da juna
Waka kwarai sani ce
Tsarata hikima ce
Rerata ba azanci
Kowa bazayi tabbaci ba
Malam yana bayani
Yara ku jini
Mai hikima kadai zaya kwance kullin zaren batuna
Kai gafara mazaga shago
Garan zuma da kura kogo
Mai hakurin kadan na tabbata ba zai zaman rashi ba
Mai dogaro ga Allah wannan ba'ayi babu shi ba
Kai de ka kara hakuri
Daure ka kara jumuri
Bawa ka rike guzuri
Kyakkyawan gamo ga Allah shine babban rufin asiri
In kaci naci, kasha nasha malam dame kafini
Toh gani na fito namiji ba mai tareni sai goga
In kaji ka iya toh ga wuri muja daga
Tsoron gamo da Allah dai nake
(Ka gama kalau lahiya)
Ni dai wannan zai sani in sake
(Sarkin waka gonar waka)
Ba yau nake tunaniba
Ba yanzu mai wucewa ba
Ban san abinda zai faru gobe ko anjima gabana ba
In kaji kida murna ce
Ba'a tambari kuka ba
Fadar ina dashi rubace
Matsoraci bazai suna ba
Ku bar ganin mutun kaskance
Ba tabbacin ba zai shura ba
In Rabbi yai nufin karuwa sai ta rigaka samun tsira
Nemi lahira bawa dan duniyarga ta zama saura
Aje abun fada mai kyau ranar da babu kai ka tsira
Daukaka nufin Allah ce
Rabbi in yaso kai dace
Gwani ya ganin dan koyo
Zai fishi nasara ko suna
Kar ka damu kar kaji tsoro
Duk cikar wuri duk taro
Nuna asalinka da shenki zai baka nasara wataran
Natsu kawai ka nemi na kanka
Dan yanzu babu mai taba baka
Kai hakuri wajen nemanka zai baka arziki watarana
Farincikin marar shi mai shi ne
Mai shi farincikin shi marar shi ne dole a rayu bangon juna
Sirrinka ya zaki sirrinka
Kar ka yawaita nuna kalarka
Maganin dukan matsalarka lillahi zaka kaiwa kuka
Ubangiji ina rokonka ba dan isa ba ko matsayina
Rabbi yafe duka kuri na
Martabar fiyayyen bayi
Rabbi yafe duka kurina
Martabar fiyayyan bayi
Rabbi yafe duka kurina
Martabar fiyayyen bayi
Writer(s): Tasiu Abdullahi Unguwa Uku
Lyrics powered by www.musixmatch.com