Lyrics

AMG boy record Alkawari damke ki rike Kar kayi wasa karka sake Jinki nake kaunar ki nake A cikin raina ka lake Zuciya begen ki take Karka damu gidan ka nake Soyayyah ce ta hada mu Rabuwar mu akwai wahala (Eh mana) Alkawari ki rike da karfi Son ki nake kiji ba da wai ba Kaima alkawari ka rike da karfi Son ka nake kaji ba da wai ba Eh kaji ba da wa Daga nesa nafara ganin ki Na yaba da irin tafiyar ki Kinyi kyau da ganin murmushin ki Kika tara maza kallon ki Nina fisu nazo, zamu keta hazo Da ganin ki nace ga kalata Kinyi kala ta Za'a wayi gari kaga munyi aure Inda rabo mu rufe ta kyaure Muyi hakuri a zama mu daure Har watarana muna a tare Ka zama ni, na zama kai Muyi rayuwar data burge kowa Data burge kowa Soyayyah ita ta hadamu Ko mutuwa ba zata raba mu Indai tazo tare zata kai mu Indan da hali rami daya a hada mu Dani dake, dani dake In zamu rayu sai dai a inuwa daya Shiyasa don shi so bai da farashi Balle a ce za'a taya shi Ya wuce duk yanda ka san shi Ko'a kala babu irin shi Dakai zanje cikin dangi Kai na zaba muyi rayuwa Eh muyi rayuwa
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out