Lyrics

Dan Musa yazo da waka (Prince Production) Masoyi yana da rana Ko babu komai shine ka debe kewa Kamar dai kace ashana Sam bashi wuta sai da taimakon makyasta Ko ranar da babu dadi Sai masoyi kadai ke taya ka kuka In kayi rashin masoyi A kiyasi ka rasa bangaren jikin ka, oh-hoho Ranar ganin masoyi, a rayuwar nan ni naga ba irin ta, la-la-la-la-la-la Allah ka ban masoyi, da zai iya hakuri da duka halika na, la-la-la-la-la-la Nasan na kanyi laifi a hukunci bai wuce kuruciya ce ba, la-la-la-la-la-la Allah ya barmu tare, in mun mutu ma a Aljannah muyi zumunta, la-la-la-la-la-la Ni ba ilimi ba Ba kudi ba Ba wani kyau ba da za'a rangwada ma Ni bani da kowa in ba Allah ba Da yayi mini rai na da lafiya na Haka shi ya tsara, in daga murya ta, inyi maku waka maganar cikin ciki na Ku so, ku so, kawai ku so masoya Ku so, ku so, kawai ku so masoya Ranar ganin masoyi, a rayuwar nan ni naga ba irin ta, la-la-la-la-la-la Allah ka ban masoyi, da zai iya hakuri da duka halika na, la-la-la-la-la-la Nasan na kanyi laifi a hukunci bai wuce kuruciya ce ba, la-la-la-la-la-la Allah ya barmu tare, in mun mutu ma a Aljannah muyi zumunta, la-la-la-la-la-la (It's Prince on the mix)
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out