Lyrics

Na dau darasi tun farkon rayuwa ta Kuma nayi karatun ta natsu gun canza akida ta (AD Music Studio) Allah sarki, duniya labari A karatun farko, nayi darasi mai tari Ni a tunani na, ilimi na zai zama jari Na tsaro komai, na zata zan kai labari Allah mai iko, shiko ya gama nashi tsari A cikin rayuwata, dole sai an dauki darasi Mai nema tashi tsaye don neman naka Rayuwar nan akawai darasi a cikin ta kamar haka Na sani duka mai hakuri zai girba abinda ya shuka A sannu, a sannu har watarana ayi masa barka In ba Allah ba waye ne zai baka ya ninka? Tun farko rayuwata har karshen ta darasi ne Ni burina in zam mai kishi Kuma yardar Allah na same shi Ya gama mini komai na roke shi Na samu abinda na so domin shi Sannan na dauki darasi A rayuwar marasa kishi Ko an taba addini bai zame masu darasi Mace yar'uwar mace Rayuwar ku tamu ce Ki zama mai hankali yar'uwa ta kar ki haukace Dubi sana'a ake yayi yanzu ba ce-ce-ku-ce Maida han-hankali wataran ke uwar yara ce Dubi halin da mata ke shiga wannan lokaci In baki dau darasi ba yanzu yaushe za kiyi? Ko a cikin siyasar mu, da akwai darasi Ko a cikin siyasar mu, mu duba da akwai darasi Wasu yan siyasar mu basa kishi mai zamu ci, zamu sha Su burin su zabe yazo ko a wannan akwai darasi Nina dauki darasi (Nima na dauki darasi) Nina karo darasi (Nima na karo darasi) (D One Mix)
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out