Lyrics

Taho na yarda da ke Zan rike kimar ki Komai zasu ce akan soyayyarki Bazana daina ba Taho na yarda da kai Lura da kema ta Taho masoyi ina kaunar ka Ganinka banyi asara ba Alamun farin ciki Yana ga fuska kika sani Na baki tukuicin soyayya Ke me zaki bani? Ranar danake ta nema tazo Yaune gaki gani Da sarka kikayi mini dauri Zuciya kika ja ni In kun ce na gaza kinfi ni Nace ba haka nan ba In kun ce na gaza kinfi ni Nace ba haka nan ba Kaso mai sanka ko wanene In dai kai tinani Ka ban-bance wa so ko kauna Tunda sunyo kaman ni Domin gudun kar misila Tai mini tafiyar shanshani Haduwar mu dani dakai Na riski abinda nai tsamani Muna tare bazan so Ace ni in rabo dakai ba Muna tare bazan so Ace ni in rabo dakai ba Tinanina abinda ka shuka Shine zaka girba Kunu ake gidan suna Mutuwa sai daka gunba Bazana raini soyayya ba Ace wani ya karba Idan hakan ya faru dani Kuce an mini zanba A rayuwa ta har in mace Ban mance ba A rayuwa ta har in mace Ban yafe ba Ba ko wani hanu yake riko Da amana Ka ban-bance cikin mata Daban da nawa suna Halaka ake fatauci da wahala Zafi da rana Damuwarka karka nuna garesu A fage na neman na Komai suka ce maka saboda ni Karka duba Komai suka ce maka saboda ni Karka duba Taho na yarda da ke Zan rike kimar ki Komai zasu ce akan soyayyarki Bazana daina ba Taho na yarda da kai Lura da kema ta Taho masoyi ina kaunar ka Ganinka banyi asara ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out