Lyrics

AD music studio Rub master Na rasa meke faruwa Kullum cikin rai da damuwa Hukuncinan naki yayi yawa Ki sassauta kinji 'yar uwa Gareni kece tudun hawa Da zani hau inyi rayuwa Ki bar fushi kiyi addu'a Allahu zai gyara dan uwa Ga mai son ki ya dawo gareki (ahh) Har sayyaya ma nayo zo in baki (ah) Sa hannu biyu ki tarbi abinki Nine naki wanda Allah ya baki Ina tayi baki saurarona Kina dauke kanki daga gurina Ko kina nufin bakya jina Dan Allah kar kiyi mini haka-haka Kin mance hudubar mamana Nace, "ko nayi laifi mu zauna" Mu fahimci juna mu auna Kar abun ya zamto haka-haka Rayuwa a tare muka tsarawa Ko baki so ban dainawa Laifina kin ji ki yafewa In samu hutu cikin rayuwa Na baka kai na Amma gareni kaci amana Daga kanka ni na daina kauna Baza ni sake yiba da kai na Nayi shiruna Duk da dai ka bata raina Kana tafe kana zagina Kar ka manta wai jini jikina Tunda har ka sani wayyo Kaima kafin ka mutu sai kayi wayyo Kururuwa da ihu gunka su juyo Allah baza ya bar ka ba kaima Allah baza ya bar ka ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
Get up to 2 months free of Apple Music
instagramSharePathic_arrow_out