Lyrics

Gajimare kullum yana sama (kullum yana sama) Tauraro ado a cen sama (ado ne acen sama) Rana a sama itace girma (itace girma) Kara hakuri farin wata Bar Rana ta karkata A daren duhu kayi 'bullowa Gari ya 'dauki take da tambura Kara hakuri farin wata Bar Rana ta karkata A daren duhu kayi 'bullowa Gari ya 'dauki take da tambura Rana ta fito gefen sama da hangenta kowa mikewa Wani kasuwa wani sai gona ga ma'aikata na farawa A sannu sannu rana take zuwa Zafin ta garin nata hauhawa Tsakiya da tazo ba natsuwa kowa yana inama ta gangara Kara hakuri farin wata Bar Rana ta karkata A daren duhu kayi 'bullowa Gari ya 'dauki take da tambura Shi farin wata da daddare ne daya fito gari ya sangalce Yara 'kana na adon gari da 'yan mata zance Haske mai wuta sannu zai wuce Bayan alfijir karku firgice Rana da tazo ya kauce Haske yakeso ya 'bantara Kara hakuri farin wata Bar Rana ta karkata A daren duhu kayi 'bullowa Gari ya 'dauki take da tambura Kaji kwarjini da haskaka fitilar daba mai kangewa Wata na nan a sama da rana kawai ke 'boyewa Mi kake nufi cikin nawa Mu muna jiran kai furtawa Hanyar 'kwarai nake hangowa farin wata nake bi na makara Kara hakuri farin wata Bar Rana ta karkata A daren duhu kayi 'bullowa Gari ya 'dauki take da tambura Bana bar batu gargadi nake duniya da rana ake nema Yardar buwayi tana ga dare hasken wata hannin dama Kan batun babu gardama Amsarka sarai shin mai kadama 'Bullo watan samanyayi sama halinsa zayin amma yaci tira Kara hakuri farin wata Bar Rana ta karkata A daren duhu kayi 'bullowa Gari ya 'dauki take da tambura Kara hakuri farin wata Bar Rana ta karkata A daren duhu kayi 'bullowa Gari ya 'dauki take da tambura Zuciya kamar zata fashe dan tunani na zautu Kullun tunanina duniya daga kukukun ta na 'dan entu Kara hakuri karka karkatu 'Dan Adam da buri zaya mutu Randa babu ni nai hutu, Rabbi sa akanka nai nasara Kara hakuri farin wata Bar Rana ta karkata A daren duhu kayi 'bullowa Gari ya 'dauki take da tambura Kai ki maidani farin wata da duhun dare bai 'boye ni Rabbi karka sata hanya ta jama'a su hallaka kareni Nasara kanima tarindini Tambaya ina kabaro tsani San Mustapha agareni farin watan da rana take jira Kara hakuri farin wata Bar Rana ta karkata A daren duhu kayi 'bullowa Gari ya 'dauki take da tambura Kara hakuri farin wata Bar Rana ta karkata A daren duhu kayi 'bullowa Gari ya 'dauki take da tambura
Lyrics powered by www.musixmatch.com
Get up to 2 months free of Apple Music
instagramSharePathic_arrow_out