Lyrics

Na aminta da ke Humaira (na aminta da kai Nasir) Zo mu zauna, zo mu saba Na aminta dake Humaira Yarda zani rikeki amana Na aminta da kai Nasir, rayuwa ka rikeni amana Shi zaman duniya hakan ne, zo mu zauna zo mu saba Kyau na al-'kawari cikawa, wanda yai wauta ya saba Indai ruwan sama na zubowa, tsirrai basa 'ki su kau fitowa 'Da na halak in ammasa rana, mantuwa baza yayo ba Sirrikan zuciya masoya, su sukeyin mallakarta Saboda so namnu sun 'kakautu, sai munyi aure zamu huta So idan yai so musulta shi, zaiyi wuya sai an wahalta Dawo madubi duba fuska, mun zame daya bamu sani ba Fadi tashi da sannu sannu, dare yakan yi gari ya waye Wanda yai dariya wataran, sai kaga shikeyin hawaye Wanda yai 'kunci a baya, bakinci nasa sai ya yaye Yadda Rabbi yaso yakeyi, ba wanda zaice bai yimar ba Kifi cikin ruwa rayuwarsa, akan tudu sam bashi yinta Ba'a sayan so koda kuddi, wanda yasaida yai mugunta Wanda yai ruko da Allah a rayuwa tasa zaya huta Rukon amana sai 'dan halali, butulu kau bazai iya ba Eh shi tauye hakki babu kyawu, abin nufi ba sai na so ba Mai haka rami na mugunta, kayishi ba mai zurfi ba Abinda ke ran dukka bawa ba zaya 'boyewa Allah ba Kyawun zato akayowa, ga mumini kuyo duba Eh 'kai 'kayi fa yana kokawa, ga wanda yakeyin shika Shuka kairi koda yaushe, abinda ba kyau karka shuka Ai duk ginin dayayo 'karko, duba ciki nasa babu toka Tanadi mai kyau aiwa gobe, duniya ba matabbata ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out