Lyrics

Oga Abdul Zango boy Is prince on the beat Baba sarkin noma ya ce, "A koma gona" Ya fahimci mun fiye son yin sharholiya Baba sarkin noma ya ce, "A koma gona" Mudaina yin magana a bisa son zuciya Baba sarkin noma ya ce, "Mu rike gona" Ya fahimci mun fiye son yin sharholiya Baba sarkin noma ya ce, "Mu rike gona" Allah kara nisan kwana Baba Numau Yau zakuga hanuna da wasika Sakon Baba Buhari nei nazo in mika Ku dakata kuji mai wasikar ta dauka A birni koh kauye wanan abu ya shafe ka Da farko lafiyan Baba Buhari Yace jikinsa ras yake ya kara kwari Masoyansa da fatan duk zakuji dadi Makiyasan yace in kun fasa tona mai asiri Baba ya ce, "A koma gona" Baba ya ce, "Mu ringa noma" Kullum mu kasance masu tsorata fama A kara dagiya cikin dare da rana Cikin wasikar Baba ya danyi azanci Abunda yasa aikin raya kasa yayai ƙaranci Matasa baba yace mun fiye lalaci Mata ku zauna a gida wanan ne inci A dan ci lokaci a jinyar Yusuf Maciciya ta hadiye kudi a ofis An aura wa Yusuf yar gidan sarauta Sanan Baba yayi yawon bin kasashe don ku huta Ba a samun wadatacen mai inji Baba Darajar man a kasuwar duniya ta karye inji Baba Baba yace baiyi bai kyale masu zamba Ku fada matsalarku wace yasani bai kula ba (babu) A shekara takwas da Baba yayai na mulki An samu nasarar yi muku titi Tsaro ya samu kowani gida na girki Daraja ta hau musamman ta garin kwaki 'Yan makaranta ai karatu don anaso Amma babu gurbin da gomnati zata baku aiki An samu nasarar koye jure yunwa Da daina abinci mai nama har gidan masu fawa Baba yace mun fiye yin sharholiya Muna magana ba tunani da son zuciya Damu kullum Baba yake kwana ya tashi Saboda jin dadinmu ya ciciyo bashi Ya magance matsla a sashi da sashi Nigeria am bata binshi da bashi A ƙarshe Baba na ma kowa fatan arziki Da sa ran kowa zai huta bayan anji jiki Baba sarkin noma ya ce "A koma gona" Ya fahimci mun fiye son yin sharholiya Baba sarkin noma ya ce, "A koma gona" Mudaina yin magana a bisa son zuciya Baba sarkin noma ya ce, "Mu rike gona" Ya fahimci mun fiye son yin sharholiya Baba sarkin noma ya ce, "Mu kama noma" Allah kara nisan kwana Baba Numau
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out