Lyrics

Eh duhun daji yazam sanadi Hawaye na yana marari Rabuwar da yazam bakin lamari Sai yaushe ne zamu gana da masoyi na rabin jiki na Duhun daji bakin sanadi Rabuwar fice a bakin lamari Buri na ganinki nai marari Zuciya ta ta zamo hadari Duhun daji bakin lamari Asa zuciya tana juriri Nidakai munyo batan fuju'a Sai yaushe gamo zama lamari Duhun daji bakin sanadi Rabuwar fice a bakin lamari Buri na ganinki nai marari Zuciya ta ta zamo hadari Allura ta 'bace da zare a duhun daji bakin lamari Hawaye ne yake ta 'bari sai yaushe gamo zama lamari Yau an rushe duka dashen da nayi dole nasha wuya (uhm, hum-hum) Kukan zuciya shine ya sakan na idaniya (uhm, hum-hum) Rabuwar mu dake ta sakan makantar zuciya (uhm, hum-hum) Zazzabi Ya sauke dukkan jiki da jini ya kewaya (uhm, hum-hum) To ni in har babu ke a kusa dani rayuwata na cikin garari Allura ta 'bace da zare a duhun daji bakin lamari Hawaye ne yake ta 'bari sai yaushe gamo zama lamari Kwana da bakin ciki nake tayi zama da 'kashin uba (uhm, hum-hum) Dadi nai bankwana dashi nai na sallama (uhm, hum-hum) Kwanciya ba dadi na kasa tsaye haka ma zama (uhm, hum-hum) Zan rabo da farinciki dake sawa nai takama (uhm, hum-hum) Rana da dare babu banbanci sarkakiya na zama lamari Allura ta 'bace da zare a duhun daji bakin lamari Hawaye ne yake ta 'bari sai yaushe gamo zama lamari Adadi na zubar ruwan hawaye bazaya 'kidayu ba (uhm, hum-hum) Farashi na tayin hauhawa saboda zubar ruwa (uhm, hum-hum) In har na tuno dake bacci sam bazai yuwu ba (uhm, hum-hum) Saidai ban mutu ba, kuma ba mai rai nake ba (uhm, hum-hum) Zuciya ta tafi tayi nisa ta wuce 'kauyuka na gari Uhuhumm Uhuhumm Uhuhumm Uhuhumm Uhm majanyin zuciya ta rayuwa ta takace (uhm, hum-hum) Kaine 'kwallin idona, aminci nakane (uhm, hum-hum) Kaine dadin ganina, tunani naka ne (uhm, hum-hum) Nabarmaka so da yarda al-'kawari naka ne (uhm, hum-hum) Acikin dadi kake ko wuya ya zamo ka rike mani al-'kawari Allura ta 'bace da zare a duhun daji bakin lamari Hawaye ne yake ta 'bari sai yaushe gamo zama lamari Eh sabanin lamari koda bamu yarda ba (uhm, hum-hum) Kaddara ce ta riga fata mai rai bai tsira ba (uhm, hum-hum) Godiya mukayiwa Allahu domin shi bai 'kimu ba (uhm, hum-hum) Salati gun Rasulullahi ma'aiki shugaba (uhm, hum-hum) Kabi sallu ala nabiyyi zababbe mai cika al-'kawari Allura ta 'bace da zare a duhun daji bakin lamari Hawaye ne yake ta 'bari sai yaushe gamo zama lamari
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out