Lyrics

Mai sona zama kinshiki nazamto danga Amince mini sai nace dake sam barka Zuciya ta kwan da binciken yar baiwa Ashe kece kika zam cikon numfashi Mai sona kazam kinshiki nazamto danga Amince mini sai nace dakai sam barka Zuciya ta kwan da binciken dan baiwa Ashe kaine zaka zam cikon numfashi Faruwa so nei abun kamar a mafarki Bayyana shi gareki yazam jan aiki Zana kare hakkinki bani son kiyi raki Ban ruwan kauna dazana sa a makoshi Na riga na fara sonka tun ran farko Adanawa nai a zuciya tai dako Aka ce giji lahira a dole na sauko Tunda dai nagane kai kamin rarashi Gun zanyi ginin gidan zago mai kwari Zanyi kofofin shigarsa tari tari Bani son a rako ni gunki jin labari Tunda dai sirrinmu namu nei boye shi Zuciya sai babu kai takan san kunci Bani son rabuwan koh gurin yin bacci Kayi mun komai a sanka banjin daci So nake, kullum na ganka ban son fashi Duk yabon danayo ce nai dai dai Zo mu zauna bani son kimin nisa dai Ambatawa nai kisa a rai nine dai Naki din nan kin zamo bugun numfashi Ni a kaunarka bani neman sauki Dan akanka ina shirin fada dasa yaki Koh a bacci nawa kai nakewa mafarki Mai shirin wara mu yayai abun ban haushi Ehhhhhh, kin gani dai ke kadai kike min kamshi Kin rike ni da gaske baki son garwashi Tunda dai a kwararafa ake jin danshi Zana zauna gunki sanki babu irin shi Mai sona kazam kinshiki nazamto danga Amince mini sai nace dakai sam barka Zuciya ta kwan da binciken dan baiwa Ashe kaine zaka zam cikon numfashi Mai sona zama kinshiki nazamto danga Amince mini sai nace dake sam barka Zuciya ta kwan da binciken yar baiwa Ashe kece kika zam cikon numfashi Ashe kaine zaka zam cikon numfashi Ashe kece kika zam cikon numfashi Ashe kaine zaka zam cikon numfashi Ashe kece kika zam cikon numfashi
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out