Credits
COMPOSITION & LYRICS
Auta mg boy
Songwriter
Lyrics
Ni ban so rabuwa ba
So ni ban so rabuwa ba
Mun hada soyayya ce ni ban so rabuwa ba
On the beat
So ya rufe ni ina ne zan sanya kaina
Kullum ina nazari ya zanyi na fanshi kaina
Kauna tana a jini tabbas so bai bari na
Da farko ina soyayya shike gudu na
Amma a yau nagane ya samu kaina
So yayi nissa, wanda ba'a ishe shi
Ya fargita ni, a yanzu ni ke gudun shi
Idan da da hali so sai in kashe shi
Soyayya soyayya soyayya
Badan badan ba
Soyayya soyayya soyayya
Bata duba min ba
Soyayya soyayya soyayya, soyayya dai
Soyayya soyayya soyayya
Anci amanata ga har ya keta mini jini
Banyi zato ba, ko a garen koko a wani
Yau karshe ce, wacce tasa so shi naki jini
A gani a kasa wanda so ya kasa nine ba wani ba
So yasan ya fada shine ya hada hanya ba daya
Ki taho mu hade komai ya dafe ba tsoro naji ba
Na baki zumar so, sai kika bani madaci
Na saki a bacci, ni kika barni a farke
Sam banyi zato ba, mai nema yayi dauke
Kin ka raba ni da soyayya, dana ganta naja baya
In na gayya miki naji ta, wanan shine karya
Babu zato ba tsamani, kuka mini yankan baya
So bai mini rana ba, tillas na fada
Nidai so bai mini rana ba, dole na fada
Soyayya soyayya soyayya
Badan badan ba
Soyayya soyayya soyayya
Bata duba min ba
Soyayya soyayya soyayya, soyayya dai
Soyayya soyayya soyayya
In kauna zata rabe, tunda alamu zata kwantanta
Ka samu sai ka rike, kai da masoyi zaku kasanta
Wanan ma kauna ce, tashi ka dubawa mabukata
Jini da hanta sun hadu
Fura da nonon ya kadu
Zama nake so mun hadu
Kida akeyi ya kadu
Ke kika bani yallon kati
Karshe sai kika ban ja ma
Ke kika bani yallon kati
Karshe sai kika ban ja ma
Lyrics powered by www.musixmatch.com