Lyrics

AMG boy record Tunda ina sanki zuciyata ta kamu Bani barinki ko zanyi kwanan tsakiyar ruwa Nifah fah ina sanka zuciyata ka saka Daga zuwanka har gashi ka dauke kowa Eh mana Da dadi ka nuna so koh da idanu Kwatancen gidanku kimin sanu a sanu Da nazo ruwa kiban hanu da hanu Kalamai na so nazo zana bajewa Jin dadin masoyi shine a kula shi Sanan yai abin yabo kuma a yaba shi Kalamanka su suke kore haushi A kaunarka zuciyata ta kafewa Gidana ki san kece farko Ki kwanta a zuciyata kiyi karko Sadakinki koh miliyan nawa zan aiko Na turo gidanku dan ai mana baiko Allah dai ya sanya alkhairi In same ki ne cikar buri Ina sanki ba gudu ba ja da baya A raina zama dake ni na shiryo Uhm na shiryo Tunanin ka shi yake deban kewa Cikin zuciyata kai daya ba kowa Amince dani da kai mun kulla Ba ranar rabo dakai kaji dan baiwa Kulawa gareka zan nuna A ranar bikin mu ai dinner Fushi in kayo dani ban jin dadi Mun shiga so a ka'ida ba kutsewa Rufe ni ki saya ni ki saya ni ki boye ni Kana da mutuncinka kalaminka ya burge ni Da kinyi shiga taki na kalla sai ta ruda ni Ni banda irinka hanyar so kai ka daura ni Idan tafiya tai tafiya toh karki share ni Kaima kasani yarda ce karka yimin rauni Na yarda dake kinga kina yi mini amfani Da dadi kalmominka suna dada dadana ni Ruwa yayi ruwa sanyi ina zaki saka ni? Ni nazama bargo ka sha dumi kaine sarki
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out