Lyrics

(AMG Boy Records) Ga sako zo amsa ki aje mini shi (Eh mana) Ga sako aje mini, in zaki tafi Nayi rubutu da tawada, farkon harafi Duk sunan ki na zuba Ba komai da ya raba Kin sanya ni nayi gudu, har nayi gumi Ciwon son ki ya bugan, duk nayi dumi Soyayyah ta ja mini Ba laifin da kikayi mini Zallar son ki zan gwada, kowa ya gani Ba zan ce ba zani ba, in zaki dani Kinsan dai dake nake Tarko naki ya rike Ga hula saka mini, kaina ya rufa Fifita kiyi mini, indai da zufa Soyayyah farin ciki Ta kau dan bakin ciki In bake bazan yi bazan yi ba, nayi alkawari Na dauka muje zuwa, nayi albishiri Kece daya nake gani Kin zo min a zamani Kin sanyo farar tufa, wanka ya hadu Mai kushe kabar fadi, don zaka kadu Soyayyah da martaba Ta sanya ina kiba Duk bayan awa daya, ke zana kira Murya taki inji ya, kin zam takwara Bana son rabo dake Rumfa taki zan fake Ba kowa a zuciya, ke daya na rika Bacin ran ki bani so, sanya a jaka Ni hauka a so nake Ba damar da zan sake Nine naki kin sani, sam kar mu rabu In ko har hakan ta zo, to zani tabu Ba fata nakeyi ba Ammah dai da fargaba Karshen so idan yazo, toh aji jiki Inko ribar sa ce tazo, toh ayi biki Har ya'ya su habbaka Wataran ko sai tsufa tazo maku, karshen lamari
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out