Lyrics

Karatu na in nayi sunan ki zana karanta Abar sona, ni nayi kiran ki zo ki rubuta Rubutu na in nayi sunan ka zana rubuta Masoyi na ni nayi kiran ka zo ka karanta Zo ka karanta mini Zo ka karanta Damina zuwan ta sai ya kore rani Dana zo gare ki babu kowa sai ni Na mallake dukan ki dama da hauni Toh kar ki canza ni Yau gaki nan gani Muna ta soyayya da ganin mu mun dace A cikin jiki ciki akwai wata tsoka In ta baci dukkanin jiki ba harka In tayo da kyau farin ciki ta baka Zuciya ce Yau na makance Ban gane komai nan zuciyata ka sace Karatu na in nayi sunan ki zana karanta Abar sona, ni nayi kiran ki zo ki rubuta Rubutu na in nayi sunan ka zana rubuta Masoyi na ni nayi kiran ka zo ka karanta Rubutu na in nayi shi ke zaki karanta Don damuwa in tazo garen zaki faranta Mai alkhairi shi ya kora hali na mugunta Kai mai sharri roki Rabbana zai gafarta Madubi na gold kike cikin yanmata Kai na rike hannu gam-gam mu shirin mu bai baci Kai ne dai na gani, na gani nike ta mita Kai ne magani-magani in na riski cuta Kin mini bazata Cikin raina kika kwanta Cikar namiji aure ni kece daraja ta Idan na shigo dakin aure kayi mini gata Ki daina fadi kisan nima nayi nisa a soyayya
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out