Lyrics

(Mai atamfa on the beat) Ke ake rika a dace Wanda bai dake ya kauce Ahmad da Nura mun ce Ke icen madaciya ce Gaskiya icen madaciya Kowa ya rike ki baya shan wuya Zurfi gare ki kin fi rijiya Kuma haka basa kure ki ba Kece cikar kowanne harafi A kan ki ba'a duba harafi Allah yasa na samu zarafi Bazan rikon abinda ba ki ba Naji dake ake ta tutiya Ke daya ce koda da kishiya Ayi fushi ko ayi dariya Sunan ki daya baza ya canzu ba Mai yin ki bashi yin tararradi Da nayi bincike a Adabi Ko masu rawuna da kallabi Basu isa su kar dashen ki ba Da kwarjini kike tagomashi Kowa ya so ki baki yada shi Cikin jini zuwa jikin kashi Duk wanda ya musa ya jaraba Rikon ki bayi jan fitar rabo Sai dai ki ja a samu shan yabo Mai rarrafe ki sa shi yayi dabo Ki kanyi tallafin marar uba Mu'amala na kanyi in dake Sannan a zuciya na tsarkake Sharri yana zuwa na tsallake Ina dake ba zana fadi ba Ni guzurin ki nayi tanadi In na rasa ki banda madadi Nayi rashin da bayi da adadi Ido ba zaya tsallake ki ba Abinda ya sani nazari Na yunkuro na doki tambari Na gaskiya ko za'a san mari Ba zaya sa na furta gaibu ba Gaskiya (icen madaciya) Gaskiya (icen madaciya) Gaskiya (icen madaciya) Ka fada in fada in fada (icen madaciya) Ka fada in fada in fada (icen madaciya) Ka fada in fada in fada (icen madaciya) (Mix golden ghost)
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out