Lyrics

Uhmm na zabe ki kin zabe ni Na amince sai ki amince min Mai sona zo muyi soyayya Na zabeka ka zabe Na amincema ka amince min Mai sona zo muyi soyayya So naji an fadi linzami ne Kai dai fadi zancen ka Shi kuma hali zanen dutse ne Ba wanda yake shakka Komai kazamo ikon Allah ne Jinka a saman dirka Ko yaushe ke daya zan nuna Kalaman soyayya zan maka Zauna gobe da labari A raina kai dai ne Zuciyana nata zata maka alkairi Ba naima jayaya Baka zuwa guna da nufin sharri Ina neman sa'a Kasuwa nason masun zubin jarri Rahsinki ya jamin nayi jinya Soyayya ko kaunaiya Da albasa mai yafi kyau suya Aguna kita kashe murya Farar yarinya mai kunya Kiyo murna da kalamai na Kece ta daya, kece ta biyu Ki tsaya daga bayana Kowa yabi dare yayo guzuri Tabbas ya biyo rana Haske da duhu daya yafi daya Sanyi makarin kuna Ki share mini kukana-aa-aa-ah Na zabe ki kin zabe ni Na amince sai ki amince min to Mai sona zo muyi soyayya Na zabeka ka zabe Na amincema ka amince min Mai sona zo muyi soyayya Uhmm-mm-mm-mm-ah Kaso mai sonka (gaske) Yafi kaso mai kinka (soyayya) Fadar alkairi (gaske) Yafi shuru ba shakka (soyayya) Bi zabin Allah (gaske) Yafi kaje kayi shirka (soyayya) Bugun soyayya (gaske) Yafi da naushi duka (soyayya) Sako zan tura (gaske) Na rasa wa zan tura bar kuka Na kamu da kauna Kaja sun ja sun sauma fata Ka jima kayi karko Samu ribar mai nema Yi shirin tafiya zanyi rako Son masu wani koshin wahala Wasu sunce ni ke ta dako Ka zamto zabina Dan haka alkawari zan ta riko Saita tinanina Harda kalamai na Zama mai uzuri guna Kar kayi zargi na So mu rike juna Ni da sonka nake kwana Ni nasan lakanin kauna Kaso aka soka fa shine Idan ka dau wani ka ajiye Kasa wani gun madadi ne Bar kuka da hawaye Ga mai share miki nine In juna muka ba yarda Duk sirrinmu mu binne Ni da soyayya nazo Jiki bar yimin gizo Yanayin yau ba hazo Kika jani ta gwangwazo Naga so da aringizo Kuma chan naga dandazo Sanki yamun rana-aa-aa-ah
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out