Lyrics

Hayya Ha-hh-hh-hh-hh-ah Zaka soni na soka burina Zanayo so dake Nima zanayo so dakai Eh so ya wuce dandanon sikari Nai dacen diya ta gari Da tabbacin lamari don bata min gada ta zare So ya wuce dandanon sikari Nai dacen da 'da na gari Da tabbacin lamari don bayayai min gada ta zare Daga yau ku kirani dan sarki a Sudan nai gamo da Qatar Da yarinya diyar asali zubinta na larabawan Qatar In ka ganta farace zuciyarta fara don naga bata ashar Na shirya zama dani da ita Bana son bacin ranta Yau nazamo majanuninta Burin danake muyo aure Ah-aa-aa-aah Kai ma dai kasani cewa kaine farkon da ba karshe Ga birnin zuciyata kuwah komai na ciki ka kwashe A gida kuwah naga dangina akanka suke ta harsashe Ni na gama duba halinka Don ba wani aibu قالبين ka Maza kuwa bakada tamka komai kaine ka tatare Da wuya a cikin su yan mata asamu kamar irin tawa Tsoron Allah da son Annabinsa shine tai damkewa Neman ilimi na addini kullum shine take yo wa Badala bata yadawa Samunta gareni dacewa Kowa kaga yayi kushewa Hassada ruhinsa ta tare So ya wuce dandanon sikari Nai dacen da 'da na gari Da tabbacin lamari don bayayai min gada ta zare Eh so ya wuce dandanon sikari Nai dacen diya ta gari Da tabbacin lamari don bata min gada ta zare Nasan wasu zasu dinga ganin ban san ciwo na kaina ba Uzuri zanyo ga masu batun domin basu fada so ba Nidai na cika burina banyo so na maso wani ba Dani daya ce yayo sabo A so yau na samu rabo Zan rayu dashi koh ba Kobo Kauye koh buka zan jure Ehh a bar baige cikin zuciya na baki amanar kaina Don koh nawa zan iya kararwa idan zan cika burina Ki lura dani makaho ne na bar miki fansar raina Gari bazai nisa ba Idan a ciki da yar Baba Ban gaji wajen tafiya ba Koda mota zan iya tsare Ahh-hh-ah lala lala Na shirya saka ka darawa ni zan share maka hawaye Idan rai yayi halinsa ka soni kamar ina raye Abunda naso wa kaina shi nake so maka ba boye Allah ka cikan burina Na mallaki wanda ke sona Domin naci ribar kauna Nasarar soyayya aure Aure ribar soyayya aure
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out