Lyrics

AMG Boy Ga amarya ga angon ta soyayyah (Eh mana) Toh ga amarya ga mayen ta an daura Toh ga amarya ga angon ta soyayyah Farin ciki ya karu sai murna Rabbana nake yin roko Ni bawan ka na dau koko Ka taimake ni in kai sako Ango amarya ga burin ku an daura Farin ciki shikenan soyayya Dubun salatuka gun manzo Dan Amina baituka sun wanzu Sa da Alihai Sahabbai yanzu Wanda bin su shi nake ko yaushe, don Allah Sanya baituka na suyi suna anfara Toh wai amarya menene ne? Gidan ki zaki je kiyi zaune Auren ga naga alkhairi ne Wallahi kayi dacen mata kai ango, da amarya ba rainawa kun dace Ango fah kaga karshen zance Amarya sai da ka tantance Ka yowa yan samari kwace Auta na MG mai waka ne, na shirya Toh amarya ga wakata ga ango Abin bida ashe ya samu Ango amarya yau dai gamu Mun zo baki kamar dangin mu Taro na gaske taron kauna, ga ango ga amarya yau kunyi aure soyayyah So ya hadaku alkhairi ne Aure kukayi yau sunnah ne Zaman da zaku yi sirri ne A da kuna ta labari ne Sai gashi kun shigo tsarin ne Jiran jira ta kare muku an daura Ku kadai ake nunawa a taron nan Kyawun amarya ya kai karshe Kota ko'ina ba kushe Ango farin hakora washe Ginin mahassada ya rushe, sai kunya Ga amarya ga angon ta, an daura Muna tayi ana nuna mu Wadan su ko suna kushe mu Bama tasu suje mu gamu Tunda rabbi shi yasan kimar mu Komai muke yana duban mu Mu masu son mu ne jarin mu Sannan abinda ke burge ni duniya, kowa nada alkhairin sa ko sharri To amarya ga angon ki Nasan kina da tarbiyyar ki Karki dinga yi mai tsaki Kisa ya dinga labarin ki Shima nasan yana kishin ki Baison abinda zai bata ki Zai kare dukkanin hakkin ki Ki dinga mai kalaman baki Kullum ya kara soyayyar ki Yau farin ciki ya karu, gun ango naga ba rufewar baki soyayyah Ahhh soyayyah
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out