Lyrics

Ki bani in baki chika chiki ba rauwa Na bayyana miki so ra'ayinane Ka bani in baka chika chiki ba rauwa Na bayyana maka so ra'ayinane A duk turare ba kamar almiski Shikuma alkuki kun aje haskene Na iso kizo ki sauka gidana Kar karace min sai wata rana Tunda kinga sonki yabi jinina A so ba kyau daga kai Dukkanmu mun gane A duk turare ba kamar almiski Shikuma alkuki kun aje haskene Na radde idona banga hazoba Na shigo da rana banyi dare ba Zana fara sa kafa tazare ba Ayi hankali dakula dukka ma'aunine A duk turare ba kamar almiski Shikuma alkuki kun aje haskene Rai da so basa jurewa kwalele Duk da dai so an sani shi da salle Damuwa in nazarin ki ya kulle Tuno laila a sharhin masoyane A duk turare ba kamar almiski Shikuma alkuki kun aje haskene A duk turare ba kamar almiski Shikuma alkuki kun aje haskene Ya kazo ka dandana mini zaki? Koko so yasa na shaki hayaki? Ni da kai a sakiyar mu da hakki In so da gaske muke yana bayyane A duk turare ba kamar almiski Shikuma alkuki kun aje haskene Ga duhu na ganshi tare da haske Dan kallo nayi tuntube har na yanke Nagani magani gunki bani na warke Akai ne zai aiki da yan bayanaine A duk turare ba kamar almiski Shikuma alkuki kun aje haskene Naji so wassu sukayi na birge Kar mu kyale ran mu yayi mana chuge So yana samun sane da irge Karshen kwatancen sa ashe cutane A duk turare ba kamar almiski Shikuma alkuki kun aje haskene Ki bani in baki chika chiki ba rauwa Na bayyana miki so ra'ayinane Ka bani in baka chika chiki ba rauwa Na bayyana maka so ra'ayinane A duk turare ba kamar almiski Shikuma alkuki kun aje haskene
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out