Lyrics

Yau kin ka bani kauna Farinciki na bai misaltuwa yanzu Ki ban ruwan zuma masoyiya Kar ki ban madaci in sha wuya Na baki zuciya na sallama Na aminta zo kija ragama Gare ni kin zamo kamar malama Kin bani ilimi cikin laluma Zubar ruwan idanu nagama Cikin jinya kin warkar dani Hangen ki nake a nesa kinyi mini nisa A sannu gashi nesa tazamo a kusa A tara duk samari zani cinye gasa Shirin da nai a kanki ya wuce na wasa Na saka kwai kin kyankyasa Sauran mu kiwo dake dani Na dan dana ashe da dadi (soyayya) Shi ne yasa nake zumudi (soyayya) A koh ina ke zanyi tadi (soyayya) Garin Kano zuwa Maradi Nine nake fadin wallahi na hade Ruwan zuma wannan ke magani Da mene zan misalta kyawun ki ne? Kira kamar kice kikayi kanki ne Mata ina ganin munin su ne Da kin shigo ciki kin haske su ne Su ce, "Akwai wasu ne" Na ce, "Akwai ki ne" Suma suna sane Wasa suke dani
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out