Lyrics

Na yi tsuntuwar soyayya Budurwa kyakkyawa Ga ni dai kamar na shirya Ina ta kakkarwa In je gareta ne ko na tsaya? Na kasa yankewa Kin yi kwarjini a idona Kina yi mini yana Aya-aya Aya-aya Da zai yiwu in san sunanki na dunga furtawa Ya zamo abin fadi na a baki nai ta nanatawa Gani nan ina ta bin sahunki ko zanyi ganewa Gidanku haka zai zaman mini sauki na dunga lekowa Koda ganinki in nai da idanu rai zaiyi kwantawa Na kamu da cuta gata 'araina ba ranar warkewa Aya-aya Aya-aya Aya-aya-aya-aya-aya-aya Aya-aya Aya-aya Aya-aya-aya-aya-aya Nayi nisa nayi nisa nayi nisa Baza na dawo ba In na furta kika ce bakya so na Bazan ki kuka ba In kau kika ce dani masoyina dadi ba zan yi barci ba Farin cikin da zana yi a ranar ba zan misalta ba Ko ba kida rawa zan taka miki bazan ji kunya ba Aya-aya Aya-aya Aya-aya-aya-aya-aya-aya Aya-aya Aya-aya Aya-aya-aya-aya-aya Idanu na suka jani Kafafu suka kai ni Zuciya tana dauki Nasan zan kice raini Zai zamto ba kamar ni Kin kirani angonki Ko nawa aka ce gareni Indai har za'a bani Zan biya sadakinki Da zan zamo miji gunki Zan kare duka hakkinki Zan zama adali a mulkinki Mai martaba a fadarki In kira ki suna sarauniya In kira ki suna sarauniya In kira ki suna sarauniya Eh-eh-eh Eh-eh-eh Ah-ah-ah Ah-ah-ah Aya-aya
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out