Top Songs By Umar M Shareef
Similar Songs
Credits
PERFORMING ARTISTS
Umar M Shareef
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Umar M Shareef
Songwriter
Lyrics
Na yi tsuntuwar soyayya
Budurwa kyakkyawa
Ga ni dai kamar na shirya
Ina ta kakkarwa
In je gareta ne ko na tsaya?
Na kasa yankewa
Kin yi kwarjini a idona
Kina yi mini yana
Aya-aya
Aya-aya
Da zai yiwu in san sunanki na dunga furtawa
Ya zamo abin fadi na a baki nai ta nanatawa
Gani nan ina ta bin sahunki ko zanyi ganewa
Gidanku haka zai zaman mini sauki na dunga lekowa
Koda ganinki in nai da idanu rai zaiyi kwantawa
Na kamu da cuta gata 'araina ba ranar warkewa
Aya-aya
Aya-aya
Aya-aya-aya-aya-aya-aya
Aya-aya
Aya-aya
Aya-aya-aya-aya-aya
Nayi nisa nayi nisa nayi nisa
Baza na dawo ba
In na furta kika ce bakya so na
Bazan ki kuka ba
In kau kika ce dani masoyina dadi ba zan yi barci ba
Farin cikin da zana yi a ranar ba zan misalta ba
Ko ba kida rawa zan taka miki bazan ji kunya ba
Aya-aya
Aya-aya
Aya-aya-aya-aya-aya-aya
Aya-aya
Aya-aya
Aya-aya-aya-aya-aya
Idanu na suka jani
Kafafu suka kai ni
Zuciya tana dauki
Nasan zan kice raini
Zai zamto ba kamar ni
Kin kirani angonki
Ko nawa aka ce gareni
Indai har za'a bani
Zan biya sadakinki
Da zan zamo miji gunki
Zan kare duka hakkinki
Zan zama adali a mulkinki
Mai martaba a fadarki
In kira ki suna sarauniya
In kira ki suna sarauniya
In kira ki suna sarauniya
Eh-eh-eh
Eh-eh-eh
Ah-ah-ah
Ah-ah-ah
Aya-aya
Lyrics powered by www.musixmatch.com