Lyrics

Kuyi hakuri Kuyi hakuri Allah zansa a farko Allah zansa a farko kan in fara bayani (kuyi hakuri) Ko ba komai kunsan shi ne wanda yayi ni (kuyi hakuri) Ya azurta ni da lafiya kun ganta gareni (kuyi hakuri) Kuma yai mani maganin komai dazai dameni (kuyi hakuri) Baiwa ya bani (kuyi hakuri) Ta kasa aka so ni (kuyi hakuri) Shine ya 'dagani duniya yau ta kalleni (kuyi hakuri) Banayin raini (kuyi hakuri) Gun wanda yafini (kuyi hakuri) Yan uwa ku biyoni (kuyi hakuri) Kuji abinda nakeyi (kuyi hakuri) Inda kuke hango ni Ba komai ya kaini wajen ba sai hakuri Kuyi hakuri Kuyi hakuri Kuyi hakuri Kuyi hakuri Duniya ce makaranta in ka ganka cikinta Wani dadi wani ko wahala zaisha a cikin ta Wani Sa zai kada wani sai ya kaiga farauta Wani dai-dai zobo wani sai ya 'daga Fanta Wani in ya huta Wani sai ya wahalta Wani baida gadon da zayasa kuncinsa ya kwanta Wani ya sayi mota tafiyar 'kasa na saka kanta Duniya a hakan a tare mu kwana mu tashi cikinta Idan mun banbanta Kar muyi 'kasaita Mun rayu ayau watakila gobe muna cikin 'kabari Kuyi hakuri Kuyi hakuri Kuyi hakuri Kuyi hakuri Haka zam mai godiya inda ka tsinci kanka (kuyi hakuri) In kana kukan rashi akwaisu dubu sun fika (kuyi hakuri) Kabar hangen sama tinda akwai na 'kasanka (kuyi hakuri) Nemo mai albarka In kabi dole a bika (kuyi hakuri) Samu da rashi in kabi Allah zai baka (kuyi hakuri) Kazamo na gari in kafadi kowa zaijika (kuyi hakuri) Alkairin naka shi zai bika a bayan ranka (kuyi hakuri) Malaman mu ku 'dauka (kuyi hakuri) Shuwagabanni dukka (kuyi hakuri) Sarakuna san barka (kuyi hakuri) Yan 'kasa kuji duka (kuyi hakuri) Komai yai zafi magani nai Allah ne kuyi nazari Kuyi hakuri Kuyi hakuri Kuyi hakuri Kuyi hakuri Ina rokon ku, in an 'bata maku (kuyi hakuri) In anzageku ba yanka a jikinku (kuyi hakuri) An 'dauki hakkin ku Allah zai saka maku (kuyi hakuri) Yana bayanku Alkawari yayo a gareku (kuyi hakuri) Ko cikin soyayya saurayi da budurwa Anyi auren sunna mata da miji kuyi duba A cikinta sana'a yau da gobe na dosheku Duniya labari (kuyi hakuri) Harshena jari (kuyi hakuri) Ya zamo alkairi Nai furuci kan tsari (kuyi hakuri) Rokon ka nakeyi har kullum Allah ka dada min hakuri
Writer(s): Umar M Shareef Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out