Lyrics

Kida Lokacin da ina dako Rayuwa ta dan rako Ko wahala tai min jiko Farin ciki ban san shi ba Hana rantsuwa na tino Rana guda naji dandano Randa nai baban gamo Labarin nake so in gino Ranar ina bakin aiki Sai naga wata tayo birki Abinda ya ban mamaki Sai ta ce, "Malam taso" Aiki nake so in biya A yanayin ta da tarbiya Ina zatonta da kyan ainiya Amman fara ce bakar niyya Ban samu abinci ba ko daya Ku bini a sanu a sanu Don jin taya ta kasance Na dauki kayan amma Ban kai ba sai da maraice Gidan su da nissa na sha Wuya a takaice Sai ta gaya mini cewa Dan dakata karka zarce Sai da na kai kayan duk tai tambayan sunana Ko da taurin kaina sai nace ki bani kudina Ka na ta ce, "Number na zan bata don wata rana" Kash na ce, "Ina gabas kina yamma" Dan Allah sallame ni da himma Kinga na gaji sosai ga jikina ya dau kirma Ta ce dani, "In yi hakuri in ci abinci kan in koma" Sai na ce, "Na gode ina zaune nai ta tinani" Shin wanan wacece? Zata zo haka nan ta tare ni Bayan na kammala cin abinci tayi mini kyauta mai girma Ta bani har number don kirata in na koma Aiko ina komawa sai na kirata don mata godiya Sai ta amsa wayata na fara zance tanai mini dariya Ai ko nai ta yabata don zatona shine godiya A hankali munyi sabo amma akwai wata matsala babba Gidansu basa sona da cin mutunci bazan jure ba To ku biyo ni a sannu ba anan kizo yai sakar ba Dan na fara tinanin rubuta waka in rerawa Lokaci baza yabar ni in bayyana labarin nan duk ba Sai ku biyo ni a sannu Sai da kai Midget Mix Kida
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out