Lyrics

A ina kuka hadu da boyayyen sirrin? Daya kama zuciya, kin ji? Allah ya hada ni dashi, boyayyen sirrin Har ya kamu da so-kauna, ko zaki raba? Daina bata lokaci, boyayyen sirrin Na zama naki tuntuni Hawan jini na, ya motsa wai mai yasa kikayi min haka, haka? Hawan ruwa na, in ya tashi ko'ina sai na jika, jika Kai kuma ka sake jikin ka, ko ka manta garen kawa ce? Har wani bata rai kake, bude idanuwan ka ka kalle ni La-la kin hau jirgin yawo Baki san sauka zaiyi ba Har wani gyara zama kike Zama kike Kaza kan ki da motsi Baki san shirme ne ba Toh lallai a ruwa kike A-ah a ruwa kike Kin sa kan ki a kan hanyar da baza ta bulle ba Kin daure kan ki cikin igiyar da bazata kwance ba Kawata ce ke, ba uwa ta ba Menene aibu na don na so wanda yake so na? Ke kika barshi yazo ba karya ba Da kin iya so bazai tsere ba Kin sarke zuciyata da rai na Kin sanya da-damuwa a kai na Kin sanya dana sanin rayuwar soyayyah Ita ce ta canza yanayi na gaba daya Wa zaya canza mini ke? Ga tambaya Wa zai bata mini ke a zuciya? Sanadin soyayyar ki na kara gane duniya Kece kika mai dani sabuwar rayuwa A ina kuka hadu da boyayyen sirrin? Daya kama zuciya, kin ji? Allah ya hada ni dashi, boyayyen sirrin Har ya kamu da so-kauna, ko zaki raba? Daina bata lokaci, boyayyen sirrin Na zama naki tuntuni
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out