Lyrics

(Beat A1 Records) Kalaman soyayya Da kaunar ka nake kwana Amfanin fitila haske Da kaunar ki nake kwana, nake tashi Ina so kiji tausayi na ko mun saba Da kaunar ka nake kwana, nake tashi Ina so kaji tausayi na ko mun saba Idan zan fadi kalmomi na soyayya Siffofin ki nake duba Dake za nayi tarayya abar so na Ba za nayi miki tamka ba Babu diyar da nake kauna da ta kaiki Ba za nayi miki karya ba Masoyin ka kayi mai so, domin Allah Koba Naira ba komai ai mun saba Yau jirgin tafiya ya zo, mu mun cilla Amfanin fitila haske Don lada aka yin sallah, masoyi na Dakai zana ci dan wake Ka koya mini na saba, da soyayya Sirrin zuci rike damke Ko'a ina kai zan nuna, ina son ka Bazan canza tunani ba ai mun saba Ina son ka Banga tare ba, turmi na gudun tabarya Ban ki gaske ba, ba kai babu daura kaya Banji zanyi ba, ha'inci a so da karya Banyi kwance ba, mene zai hanani zarya Bani tagumi, mai rai zai ishe maraya Kai duniya, tunani nake na baya So da alkawar, mu damke muje mu kurya Babu lafiya ban gan ki a kusa na ba Naji na gani, da kai zanyi rayuwata Bani ba wani, sirrin zuci manufa ta Zanyi gwangwoni, indai har kayi mini rata Fitar gani, ido ka ciran makanta Sani dariya, daure kayi mini gata Kaini-kaini ni da kai zan wuce makwanta Kara kyan gani, a so kar kamin mugunta Nawa naka ne, bazan barka ko dare ba Naso kiji tausayi na a soyayya, koda nayi miki laifi Da kaunar ka nake kwana nake tashi, ka saurari kalamai na Da kaunar ki nake kwana nake tashi Ina so kaji tausayi na ko mun saba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out