Lyrics

So na ne fah On the beat Ni kece cikon mafarki Zan bude sirrika Kauna ce ta samu gurin a cikin ruhi ta habbaka Burina na, na zama rumfa rana in tare maka Komai in kana bukata guna zana yi maka In dai har kanki ne bana tamkar war wara Kyale duk wa'inda ke cewa zanyi maki yaudara Ni kai ne cikon mafarki na dauri dammara Soyayya ta gaskiya ce zamuyi ba jiran-jira Inda abun da zan sadaukar kan so ke zana ba In bake ba zuciya ta zatayo maraba Yau ka tabbatar da lallai nice ba wadansu ba Soyayya ruwan zuma bude bakin ka in zuba Kin gama komai soyayyar a gaskiya kinyi min Masu bida ta munyi ja in ja suka ce sun bar min Gobe da nisa shakar iskan madara sai rani Mai mana kuri mun san kauyen kuma mun san birni Duba madubi kyawun ki yana dada janyo kallo Kar kaji komai duk inda bayana sai na bulo Masu kwallailai sun rodaka sun rasa harshen gwalo Kowa ya taba min kai zan haka sai na cillo Zan maki wargi mai so ya zama gwanin rarrashi Ka iya wanka in ka motsa haka sai dai kamshi Daina yabo na kar murna ta hana nai numfashi Alkawari nayi nidai ban maka abun ban haushi San ki da dadi Ai ka zama sha daka turmin danya Mai mana kaudi Ai baya gaya mana girman kwanya Kar kiji komai nisan jifa kasa sai ta dawo Muyi hadaka in ka kawo haka sai na kawo Jeki ki dawo Bani sirrin ciki sai dai hanji Barsu da bawo In ka motsa a jiki sai naji Share batun duk wani mai son ya mai na yankan baya Naga kalaman soyayyar gaske ta fara bullo Wanda ya kushe man ke sai munyi zare ban kwarya Kar kaji komai duk wanda yake kwado ya san gaya Mix kobincus Ni dake zanyi soyayya A rayuwata Me zai sanya in bar ki? Masoyiyata Kai daya ne kake mulkin zuciyata Kake maganin dukkan damuwata Kin zamto cikon buri, sahiba ta Gidan duniya kece samuwa ta Miye zaya dame ni? Kana kusa na Idan ba ka na rantse sai makabarta
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out