Lyrics

Zamu tafi, ni dake ko'ina zamuje Na rike so da kauna abadan da'iman Haske ya fito Waye zai tare? Daga tauraruwa Mai kyan anbato Haske ya fito Waye zai tare? Daga tauraruwa Mai kyan anbato Nai wata tsintuwa, mai kyawun gani Daga kalo daya tai mun kwar jini Zane na nayo tun ranar gini A tsaya ya huce, ke sanya rabon wani Dama zaki soni Kauna zaki bani Da duk hankali a kai naki zan karkato Ehh toh bar hanzari Kana kiyo shiri Dan kin sam guri Sai dai jinkiri Mai noman wuri Ke tsoron fari Na boye iri Domin banzari Yau kin cimma buri Sai ki rike sirri Kokin so da ji da kuka zan kanfato Haske ya fito Waye zai tare? Daga tauraruwa Mai kyan anbato Nashiga yanayi So yayai min tayi Da kudi na sayi Babban matsayi Tinanina nayi Bashi da rairaiyi Yaya zanayi? Zuci da tausayi So yazo da sauyi Zamani da juyi Yaki zuciya a so da fito na fito Haske ya fito Waye zai tare? Daga tauraruwa Mai kyan anbato Kauna ta shigan jiki tai mun mamaya Nashiga yanayin daya wuce ayi tambaya Fuskata, jikina duka sun sausauya Na gaza gane komai ina gwa-gwarmaya So dai shi ya sanya Na zamto maraya Da kun gan ni kunga majanunin so ya fito Ah-hh-hh-ah-ah-ah Ah-hh-hh-ah-ah-ah Taka a sannu kinji sarauniya Mai kyan ido, kuma ga kwalliya Nayo kiranki da zinariya Tauraruwa ta mata dawisiya Mai tarbiya Sannu sarauniya Daga an gano ki annuri ya fito Haske ya fito Waye zai tare? Daga tauraruwa Mai kyan anbato Ya Allah tsare mu sharrin mai ziga Mai baki na jaba tsini yana bindiga Ita ba rariya ba sai faman zazaga Ni bana shiri da mai bakin ganga Tace karta soni Toh yanzu ga akini Ita ko ta kafe a kaina tafi anbato
Writer(s): Isah Ayagi Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out