Lyrics

Ayagi record Karo arziki ta"alah Muci mu sha har mu bayar Mu siyo sitira mu dinka Mu fito ku ma a gan mu fes-fes Masoyan mu suji dadi Su koh magauta su kwan da haushi Bakin ciki ya hana su barci Ban san dadin aboki ba ga amin na wuyar nema Sarki hulawalazi lilahi Albarkacin Rasulullahi Allah ka bamu ba don mu ba Allah kaba wa duk mai ba mu Kwato mana hanun mai hana mu Koda yaso koda bai so bah Shi arziki nufin Allah ne Yana isaarka ko kana zaune Ko makiyinka sam basu so ba Toh kai mai gina ramin mugunta Ka gina shi na dai dai wuyanka Ina sanar dakai mafarauci, kafin kaga biri biri ya ganka Sirri sai mai shi Mai aike zai koma kun shi Kunyi sharrinku, ga wanda Allah yake san shi Yaya gara takanyi da dutse bazai ciyu ba sai kallo Ke duniya rawar yan mata Na gaba sai ya koma baya Mai gaskiya ashe ya huta Kunya tana gurin mai karya Munafukai suna ragaita Mun gaba mun baro su a baya Mai hassada garen nan-nan gankata kan ka aza maka kaya Mu godiya ga muke kowa ya ganmu bama bulayi Kowa ya kama aikinsa fagen nawa bani yin wasa (yin wasa) Sai an dasa ke tasa Da zance na zere mai gasa (gasa) Ashe a duniya munka hadu a duniyar ga zamu rabu Inka zageni kan wani ka daura kafin ka anyi yafi dubu Amma gani ras Gani fes Gani chass chass Ku kun fadi kasas War was Mun biyoku da ass Munata godiwa rabbana Rana hantsi na safiya Kyautar da yayai min na bayyana Yaban masoya a duniya Sunana ya zagaya duniya Har tsalaken Nigeria Sakon ku nan na zuwa ai masoya ni naku ne Kunce dani yanzu baku ji na sosai wai me yafaru ne Ne koh nace muku ina shiri ne na tsaba domin ku ne Manyan masoyana na ko ina Isah Ayagi naku ne Kabiru Aiyuni na Maryama masoyi asali tun usuli Ina da Adam Sara A ko ina bai kaura Akwai Sadiq Sofa nawa daban yake kan saura Ina da SY dan sunnah yazo da babbar gara Da Abba dan fulani mai adedeta sahu ina yin gaisuwa Akwai Habu gaye nawa masoyi ne ba gyra Ina da alhaji K Arrow masoyi ne dai shima Da Bandirawo masoyi nei nai godiyar ban girma Da Laisamin mai adedeta na isamu nai jinjina Akwai Biggie na garin Legas da jinjinar ban girma Akwai Najin mai kunji masoyi nai girman Ina da MK Sardauna masoyi ban manta ba Da Abba Isah na freedom masoyi ne bawai ba Ina da FKD na Ibadan da jinjinar ban girma Akwai Muhammad S Kabobe da jinjinar ban girma Rabi'u aci balance nawa na jinjina na yo ma Akwai Rahinatu yar Niger bafulatana tayi min Da Sani city Niger nawa na jinjinar girma Abubakar na Isah Ayagi nai jinjina har kai ma Sauran masoyana na fadin duniya da jinjinar ban girma
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out