Lyrics

Na fara soyayyah, jin dadin ta ya sa ina zance Kamar zana susuce, idan babu ke sai na hau zance Bayanai na soyayyah, mai yi nata ne zaya bambance Nima gani na afka, idanu na basu gane kowa sai ke daya Ni dai gaskiyar zance idan baki nan gara bana nan Ina za na tunkara? Idan aka ce baki duniyar nan Fada ne na kan kara, kece zuciya ta ruhin nan Bazan canja niyya ba, kuma ba mai canja ra'ayin nan Idan kinga na bar ki, numfashi ya daina harbawa gaba daya Soyayyah halitta ce, a kan son ki kai za na kaskanta Ke kin zama yar lele, kiyi min rigima zana jure ta Kulawar da zan baki, misali na yaya da yar auta Bazan gaza gwiwa ba, fagen kyautatawa da ririta Idan ran ki ya baci, ni zan lallaba ki ya sassauta Nagode Allah na, da zai bani ke matsayin mata Ni ke zanyi wa bauta, koda rayuwa zata salwanta Fada wajibi ne a so, idan munyi toh sai sulhunta Mun zama hadin Allah, muyo rayuwa haka ya hukunta Masoyi abin kauna Masoyi abin so ne Na sha soyayyah (na sha soyayyah) Dadi soyayyah (dadi soyayyah) Haahh, ummm (Shano style mix) (TK Adam ne)
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out