Lyrics

Hadin Allah babu mai iya rabawa Yusuf da Ameerah, Allahu ne ya hadawa Hadin Allah babu mai iya rabawa Yusuf da Ameerah, Allahu ne ya hadawa AD music studio Kyauta wadda ba'a tsanni, tana zowa daga masoyine Wanda yasan soyayya, kuma ya damu da mai sonshi Alkawari shi kayane, ina fatan kin gane Ameerah kar kiyi wasane, Yusuf yace yana sonki Zuciya duka ya baki Da rayuwa ya mika maki Yace ba wata tamkarki Dan Allah kar kiyi mamaki Kullum yana kan shaida maki Yace a ransa yake jinki A gurinsa ne naji labarinki, halinki hali na kirki Ameerah baiwar Allah Ameerah tasan Allah Ameerah mai bautar Allah, da kaunar Manzon Allah Amerah Yusuf nakine Ameerah Yusuf masoyinki ne Ameerah Yusuf mai jinki ne, a cikin ranshi Oooh Oooh Ko a cinkin ayarin mata Ameerah ke ta dabance, kwalliya ga kyau zuwa tsafta Komai naki na daban ne Kina da Yusuf me zaya dameki In babu shi na shaida komai kika ce ya siyi miki Bayayi da wasane A gareki Yusuf aboki ne Sannan amini ne, wani bangaren dan uwane na jini, Ameerah kin gane A gareki shi garkuwane, mai yaye damuwane Mai dauke duk fushine, sannan fa maigidane Allah ya nunan aurenku Inzo bikinku in ta taku Harma da sunan 'ya'yanku Ameerah Yusuf kwarrarene Allah kaine kake cika buri Ga bayinka nan kan tsari Burinsu su raya sunnar, habibinka haske nuri Ya Allah kasa masu alkhairi Sannan kasa su a kan tsari Yusuf Ameerah masoyane, masu niyyar alkhairi AD music studio
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out