Top Songs By Moussa Yaro
Credits
COMPOSITION & LYRICS
Moussa BOUBE HAROUNA
Songwriter
Lyrics
Jirgin so yau zai tashi
Mai sona dake zan koma gida
Jirgin so yau zai tashi
Mai sona tare zamu koma gida
Burina muyi soyayya
Nai sa'ar mai alkunya
Diyar girma mai tarbiya
Zan jajirce nasa niyya
Na aure ki
Gaki a dakina na maishiki amarya
Dan samari mai ado zubin dan Fulani
Zan biyaya gareka me kake so nayi gani
Nayi fata kazam mijina kaga gani
Zanyi murna duk randa ta kasance
Kazam uban 'ya'ya na nasara ce
Kai ka yanta ni har nazam autar mata
Kin ciren damuwa taho garan yar uwa
Bani ji bani gani akanki nai rantsuwa
Ke nake so kin bani sabuwar rayuwa
A zuciyata kinyo dashe naso
Nazo gareki fushin ki bani so
Kece na zaba
Domin na baki dukanin gata
Jirgin so yau zai tashi
Mai sona tare zamu koma gida
Nasani baka sani inyi kokawa
Ko fushi nai kake sakani darawa
A daura aure gidanka zanyi tarewa
Zaman amana gidanka nai niyya
Saboda kauna zan maka jar miya
Kasha ta kayi santi ka kara
Haka nai yo fata
Na amince
Nima na amince
Na makance
Dakai zan kasance
A so bazamu yi rabuwa ba
Koda anyi niyya
Ranan dakai nayi mafarki a so
Na yaba kyauta da tukuici na so
Farin cikin mai sone ya samu mai gata
Jirgin so yau zai tashi
Mai sona dake zan koma gida
Jirgin so yau zai tashi
Mai sona tare zamu koma gida
Writer(s): Moussa Boube Harouna
Lyrics powered by www.musixmatch.com