Lyrics

Eh boye abin cikinka to karda ka tona Ka kuka waya kyautu damkawa amana Wani ka bashi bai gudun aika hiyana Kula gaban ka baya ta barka ka auna Ance rabon maza Baya shiga dawa Kuma so gamon jini Dangin shi mutuwa Wasu sunyi sun gani Sun nemi afuwa Ni nau na tsansane Zan kauda tsakuwa Eh masu shiga shara kan hadari suke Watakila a yarda Shi kuma damake raina kama yake Kaga ya rike sanda Shi hadarin sama in kaga an fake Da ruwan cika randa Duk maganar baka kan adadi take A tsakar wasu suda A gani a baya-baya kaine daga fari Na kasa shi ya boye mu mun wuce gori Mai biya karya-karya baya kafa jari Mai iya kai makwarya shike rufe sirri Fatan arziki Sai dan arziki Mu mun karkare, har an sha biki Tsarkin zuciya shine kyan jiki Ni na bayyana an ban mallaki Da haka duniyar take aika misali Wani abun akanyi ko babu dalili Wani ka kan shi bai hawa ko a sikeli Ka iya naka bai wuyar warware kulli
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out