Lyrics

Fatan alkairi zanai Gwanja ne Dan suji in sun kayo na'am Dai-dai ne In Allah yayi sunka ki Zance ne Haba, gata Sunusi yar Adam Sadiya Mai son tuje tushiya tafi kunya Sadiya ki dan tsaya daga baya Naugawasa magani aje dinya Masu duhun bakin ciki, suji kunya Wanda ya furta bai dake, yaci baya In Allahu ya nufa Sadiya Ya baki Sunusi yan uba, suji kunya Yi da rashin yi na rabbi ne Basu ba Nace Kai Sadiya kin zamo cidda Hana sauri Mar maza gane makiya, dada tsari Kinfi dubu uwar dari Cika kuri Sadiya wa yace dake bake ba Muma sai muce dashi bashi ba Nace, "Shiga ki keta yan uba" Daga danba Dan kirki gunki Sadiya Ba daga nan ba, kai Sadiya Adam Rike Sunusi gam-gam Sadiya kin zam Kamar ruwa na zam-zam In ta miki dadi Sadiya akame kam Sadiya share ruwan idaniya Tina baya Daura bazarki Sadiya Kiyi rawar ki Kina da maganin fushi Sunusi naki Mance fushi na makiya Gaba takai ki Idan goma tazata kai Kashe dayar ki Ashe sai ruwa ya sauka ayi shuka Ki zamto kamar dage mai jire duka A gaza gane kanki, kin zama sarka Dauki fara da koriya, tafi ki sirka Karki zamo candle sai kin konu ki haska Nace ki rike naki dan uba Ya rike nasa Ki taimaka wa yan kasa Karda ki fasa Rabbi yakai mu ran bikinki Da bikin sa Zan yi rawa a ran bikinki Sadiya Albishirinki Sadiya kiji batuna Yi addu'a cikin dare bita da rana Take kafar bazan baci, dan yaji kuna Ba amfanin dazai miki Ni a gani na Dan in mun tafi lahira Bashida rana Nan zayi ta kansa Kiyi ta kanki, inyi ta kaina Maza-maza mance dashi Sadiya kiji batuna Sannu-sannu farar majingina Sadiya bango Dan kita zaman farin ciki Na miki dango Rabon kwado ko ya hau sama Toh zaya dirgo Nace Sunusi yazamo naki Ke Sadiya Sunusi kuma kin sani yanada 'ya'ya Sadiq da Nihal maza ki musu rana Faruk da Iman zaki iya musu rana Domin suma wata ran su miki rana Ki kwantar da hankalinki Sadiya Ki kwantar da hankalinki Sadiya Sama
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out