Top Songs By Umar M Shareef
Similar Songs
Credits
PERFORMING ARTISTS
Umar M Shareef
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Umar M Shareef
Songwriter
Lyrics
Mun zama hanta da jini, soyayyace tas kawa
Soyayya kan gaskiya abadan bata mutuwa
Mun zama hanta da jini, soyayyace tasawa
Soyayya kan gaskiya abadan bata mutuwa
Hanuna rike, yan mata ke nayi hari
Zan zauna dake, alkawari ni nayi shiri
In har babu ke kwara ku kaini cikin kabari
Nai dogon nazari nagane hadinmu dake shi zaifi daidai
Nai dogon nazari nagane hadinmu dakai shi zaifi daidai
Mun zama hanta da jini, soyayyace tasawa
Soyayya kan gaskiya abadan bata mutuwa
Baki ke fada, kune ko sai dai yajiya
Wanda yake bida, sam baya saurin gajiya
Kun jadada na yau din ai shine na jiya
Tarago fa cikin tafiya, kaine ba chanji a gareni nidai
Tarago fa cikin tafiya, kece ba chanji a gareni nidai
Mun zama hanta da jini, soyayyace tasawa
Soyayya kan gaskiya abadan bata mutuwa
Banda kamarki ni, a baki da zuciya
Kowa yasani, mun zamto daya
In an baki ni, sam sam baki shan wuya
Zaki kula dani, nima zan miki gaskiya
Zo mu kwatanta tunda Allah sarki shine yafi daidai
Mun zama hanta da jini, soyayyace tasawa
Soyayya kan gaskiya abadan bata mutuwa
Kazama zakara
Da kai nayi fariya
Matakin nasara
Ance gaskiya
Duk ka tatara su suka gyra ma tafiya
Waye zai taro gabanka inai mai ban gajiya?
Ni na amsa kira nazo gaka masoyina daidai
Ke nafi kauna yan mata kinsan haka
Nima kai nafi kauna a gayu kasan haka
Tabbas komai nawau daukawa bance ya haka
Nima komai nawau dauka masoyina nabar maka
Ko ra'ayinmu guda domin mun zamto hanta da jini
Mun zama hanta da jini, soyayyace tasawa
Soyayya kan gaskiya abadan bata mutuwa
Mun zama hanta da jini, soyayyace tasawa
Soyayya kan gaskiya abadan bata mutuwa
Lyrics powered by www.musixmatch.com