Lyrics

Bude cikin zuciya ki jefa ni In na shige sam kar ki fidda ni Bude cikin zuciya ka jefa ni In na shige sam kar ka fidda ni Dan mazari a kira gwanin rawa In ya fito tilas a yo kalla 'Yar makaranta na fi so kunga Bani shiri da diyar dake talla Fidda gwanin ki kice ba gani ba Je a gari kiyo shela Nine na zama zabin ki Daurin auren mu nayi dauki Taron auren mu za'ayi bikin Da ba a taba yi dangin mu Na guji samarin zamani sun sanya budurwa tayi kwalla Mai kwadayin sabon zani itace gayu ke yiwa illa Nayi addu'an samun miji nagari kullum in nayi sallah Dakai ya hadani a duniya Rayuwar mu muyita mu sha miya Nayi fata ko a lahira mu zamo tare a cikin aljannar mu Taro da kwabo in har na samu ke zan ba ajiya Domin yin amfani gare mu kai har ma da iya Albarkar sa tasa ki dube mu yau mun zarce jiya In mun bisu cikin lamarin mu muyo nasara Hannu kyauta shike samu in har ya tara Mudai sai fa mu kara godewa ba abinda yake damun mu Rikita-rikita nai alkawari Bazan sanya ka kuka ba Kwarin gwiwa na karama Bazan sa kayi rauni ba In mun samu mu gode rashi ba zai sa muji komai ba Allah shine ya bamu In yaso baya bamu Sai yanda kaso kake yi alkhairi Allah ya sada mu Bude cikin zuciya ki jefa ni In na shige sam kar ki fidda ni Bude cikin zuciya ka jefa ni In na shige sam kar ka fidda ni
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out